Makiyaya sun miƙa wa ƴan sanda ɗan uwansu, Jabir Nuhu, bayan ya kashe manomi

Makiyaya sun miƙa wa ƴan sanda ɗan uwansu, Jabir Nuhu, bayan ya kashe manomi

  • Wasu makiyiya sun dauki dan uwansu mai suna Jabir Nuhu sun mika shi hannun rundunar yan sanda
  • Sun yi hakan ne bayan Nuhu ya daba wa wani manomi wuka a cikinsa kuma hakan ya yi sanadin mutuwarsa
  • Makiyayin mai suna Cindo ya gargadi Nuhu kada ya kutsa masa cikin gona amma sai da ya shiga hakan yasa ya kama shi da dambe

Jihar Gombe - Makiyaya sun mika wa yan sanda dan uwansu mai suna Jabir Nuhu kan zarginsa da kashe wani manomi a kauyen Bada da ke karamar hukumar Dukku a jihar Gombe.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa lamarin ya faru ne a makon da ta gabata bayan rashin jituwa ya shiga tsakanin Nuhu mai shekaru 15 da wani manomi saboda zargin kutsa masa gona.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Neja ta rushe gidan wani kasurgumin mai garkuwa da mutane a Minna

Makiyaya sun miƙa wa ƴan sanda ɗan uwansu, Jabir Nuhu, bayan ya kashe manomi
Makiyaya sun miƙa wa ƴan sanda ɗan uwansu, Jabir Nuhu, bayan ya kashe manomi. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

A cewar majiyar, manomin ya fusata bayan Nuhu ya ki bin umurninsa na cewa kada ya kutsa masa ta cikin gona, hakan yasa ya kama Nuhu da dambe, shi kuma ya daba wa manomin wuka a ciki.

Cindo ya ce ga garin ku a yayin da ake hanyar kai shi asibiti a Dukku kamar yadda ya zo a ruwayar Daily Trust.

An tuntubi mai magana da yawun yan sandan jihar Mallum Buba dangane da lamarin amma ya bukaci a bashi lokaci ya yi bincike.

Bai mayar da martani ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Jigawa: An kama makiyayi da shanunsa 73 da awaki 14 saboda kutse cikin gona

A wani rahoton, 'yan sanda a jihar Jigawa sun kama wani makiyayi mai shekaru 25, wanda aka zargi ya kutsa cikin gonakin wasu ya lalata kayan gona na N200,000 a kauyen Takatsaba da ke karamar hukumar Suletankarkar a jihar.

Kara karanta wannan

Yan ta'addan Boko Haram 17,000 suka mika wuya kawo yanzu, Kwamdanda Operation Hadin Kai

Jaridar The Guardian ta ruwaito ASP Lawan Shiisu, mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Jigawa ya tabbatar da afkuwar lamarin ciin sanarwar da ya fitar a Dutse, ranar Alhamis.

Shiisu ya kuma kara da cewa yan sanda sun kama shanu 73 da awaki 13 da suka kutsa gidan wasu gonaki a ranar 10 ga watan Oktoban shekarar 2021.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: