Kungiyar mata 'yan jarida sun koka kan tsadar rayuwa, sun mika bukatarsu ga gwamnati

Kungiyar mata 'yan jarida sun koka kan tsadar rayuwa, sun mika bukatarsu ga gwamnati

  • Kungiyar mata 'yan jarida ta bayyana kokenta kan yadda tsadar abinci da rayuwa ya addabi kasar nan
  • Kungiyar ta roki gwamnatin Buhari da ta taimaka wajen sanya hannu a samawa 'yan kasa sauki a bangarori daban-daban
  • Hakazalika, kungiyar ta koka batun yawaitar cin zarafin mata, inda tayi kira da kafa kotunan iyali a kasar

Nasarawa - Kungiyar mata ‘yan jarida ta Najeriya ta bayyana damuwarta kan yadda ake ta fama da matsalar rashin tsaro a kasar da kuma tsadar kayan abinci da iskar gas da dai sauransu.

Ta bayyana korafin ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakatariyar kungiyar, Helen Udofa a karshen taron NAWOJ NEC da aka gudanar a garin Lafia jihar Nasarawa tsakanin 3 zuwa 5 ga watan Nuwamba 2021.

Kara karanta wannan

Miyetti Allah ga FG: Don Allah ku ayyana 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda

Kungiyar mata 'yan jarida sun shiga damuwa kan saboda tsadar rayuwa
Kungiyar mata 'yan jarida | Hoto: www.theunionnigeria.com
Asali: UGC

Kwamitin sanarwar ya bayyana Dorathy Nnaji (PhD) a matsayin Shugaba, tare da Rose Elishama a matsayin Sakatare da Nene Dung a matsayin mamba, Independent ta ruwaito.

A taron da shugabar kungiyar ta NAWOJ na kasa, Kwamared Ladi Bala ta jagoranta, an tattauna batutuwan da suka shafi kungiyar da kuma halin da kasa take ciki.

Sanarwar ta kara da cewa:

“Batun rashin tsaro a kasar nan ya dauki hankalin NEC inda ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta karfafa tsarin tsaro na kasa domin magance matsalolin tsaro a sassan kasar nan.
“NEC ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta duba tsadar kayan abinci, iskar gas, kayan gini; domin rage tsadar rayuwa ga yan kasa a kasar.
"NEC ta nuna takaici kan yadda ake ta samun karuwar cin zarafin mata tare da jaddada bukatar tabbatar da aikin kotunan iyali domin tabbatar da adalci ga wadanda abin ya shafa.

Kara karanta wannan

Hukumar NYSC ta koka kan kudin abinci: N650 ga 'yan NYSC, N1000 ga fursunoni

Sama da gidajen man Kano 50 sun rufe yayin da karancin man fetur ke kara kamari

A wani labarin, Mazauna babban birnin Kano da fasinjoji daga garuruwan da ke kusa kamar Wudil, sun makale saboda rashin samun ababen hawa sakamakon karancin man fetur a jihar.

Tsoron karin farashin man fetur da ake sayar da shi kan Naira 165 ya shafi masu ababen hawa da harkokin kasuwanci a jihar.

Daily Trust ta gano cewa sama da gidajen mai guda 50 ne aka rufe daga Wudil zuwa Kano kan babbar hanyar tarayya ta Maiduguri, inda aka ga gidajen man fetur shida ne kacal a bude.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.