Zamu Janye Malamai Daga Yankunan Da Ba Tsaro, an Halaka Guda 800, Ƙungiyar Malamai Ta Ƙasa
- Kungiyar malamai ta kasa, NUT ta koka akan rashin tsaron da ya ke ta hauhawa a yankin arewacin kasar nan inda ta ce yanzu haka an halaka mata malamai 800
- Kungiyar ta yi barazanar janye malaman ta da ke wasu kananun hukumomin da ke jihohin arewa maso yamma saboda garkuwa da mutane da sauran ta’addanci na yankin
- Shugaban kungiyar, Dr Nasir Idris ne ya bayyana hakan a ranar karshen makon da ya gabata a Abuja, inda ya ce hakkin gwamnatin tarayya ne kula da rayuka da dukiyoyin jama’a
Abuja - Kungiyar malamai ta kasa (NUT) ta koka akan yadda rashin tsaro ya ke hauhawa a kasar nan, inda ta ce kungiyar ta rasa malamai 800 a yankin arewacin Najeriya kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Ta kuma yi barazanar janye malaman ta daga wasu kananun hukumomi da ke kasar nan a arewa maso yamma saboda hauhawar garkuwa da mutane da sauran harkokin ta’addanci bisa ruwayar Daily Trust.
Shugaban kungiyar NUT, Dr Nasir Idris, ya bayyana hakan a wata tattaunawa da manema labarai su ka yi da shi a Abuja a kwanakin karshen mako.
Kamar yadda ya ce, aikin gwamnatin tarayya ne kulawa da rayuka da dukiyoyin jama’an da ke kasar nan.
Ya ce akwai malaman da suka ki yarda a sace dalibai a bar su
Dr Idris ya bayyana cewa:
“A yankin arewa maso gabashin kasar nan, mun rasa malamai 800.
“A bangaren arewa ma so yamma, an yi garkuwa da wasu malaman mu da yaran su saboda wasu malaman sun nuna cewa ba za su yarda a saci dalibai a bar su ba.
“Duk yankin da gwamnatin tarayya ta kasa samar da isasshen tsaro, za mu bukaci malaman mu da su janye su hakura da aikin.”
Idris ya kara da kira ga gwamnati akan amincewa da kai shekaru 65 kafin malami ya dakata da aiki da kuma kwashe shekaru 40 malami ya na aiki da kuma sallama mai kyau.
A cewarsa, yanzu haka malamai da dama sun kaura daga azuzuwa saboda rashin kulawa da gwamnatin tarayya ta ke nuna mu su.
Kamar yadda ya ce, rashin kular ce ta ke tursasa malamai su na hakura da aiki a karkashin kananun hukumomi, jihohi da gwamnatin tarayya.
Abin da yasa har yanzu Nigeria bata zama ƙasaitacciyar ƙasa ba, Ministan Buhari
A wani labarin daban, Ministan Kimiyya da Fasaha, Ogbonnaya Onu, ya ce har yanzu Nigeria bata cimma babban matakin da ake sa ran ta kai ba a lokacin samun 'yanci saboda an yi watsi da irin halayen mazajen jiya da suka kafa kasar.
Shugaban CAN: Farashin kuɗin fansa ya ƙaru a Kaduna sakamakon rufe hanyoyin sadarwa da gwamnati ta yi
Ya yi wannan jawabi ne a babban birnin tarayya Abuja wurin wani taro da kungiyar 'Yan Kabilar Igbo ta shirya don karrama Rear Admiral Godwin Kanu Ndubuisi (mai ritaya), Daily Trust ta ruwaito.
Onu ya ce ya zama dole 'yan Nigeria su zama masu gaskiya, aiki tukuru da riko da halaye na gari idan suna son ganin kasar ta zama tauraro tsakanin sauran kasashe.
Asali: Legit.ng