Da duminsa: Babban rashi ya taba Sanata Abdul Ningi a Bauchi

Da duminsa: Babban rashi ya taba Sanata Abdul Ningi a Bauchi

  • Allah ya yi wa mahaifiyar tsohon Sanata mai wakiltar Buachi ta tsakiya, Abdul Ningi, rasuwa a jihar Bauchi
  • Hajiya Abu ta rasu a ranar Lahadi a garin Ningi da ke jihar Bauchi bayan gajeriyar rashin lafiya da ta yi fama da ita
  • An yi jana'izar ta kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar a fadar Sarkin Ningi, Alhaji Yunusa Muhammad

Ningi, Bauchi - Mahaifiyar tsohon sanata mai wakiltar Bauchi ta tsakiya, Abdul Ningi, Hajiya Abu ta rasu a ranar Lahadi a garin Ningi bayan fama da gajeriyar rashin lafiya, Daily Trust ta wallafa.

Daruruwan masu makoki tare da ta'aziyya sun bayyana daga ciki da wajen jihar Bauchi. Sun hada da Gwamna Bala Mohammed, Sarkin Ningi da fitattun 'yan siyasa wadanda suka halarci jana'izar ta a fadar Sarkin Ningi, Alhaji Yunusa Muhammadu Danyaya.

Kara karanta wannan

Miyetti Allah ga FG: Don Allah ku ayyana 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda

Da duminsa: Babban rashi ya taba Sanata Abdul Ningi a Bauchi
Da duminsa: Babban rashi ya taba Sanata Abdul Ningi a Bauchi. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

A yayin ta'aziyya ga Sanatan, Gwamna Mohammed wanda ya jagoranci manyan jami'an gwamnati zuwa gidan rasuwar, ya kwatanta mamaciyar da babban jigo wacce ta yi rayuwa tagari.

Ya yi addu'ar Allah ya sanya ta a Aljannar Firdausi kuma ya bai wa iyalan ta hakurin jure wannan babban rashin, Daily Trust ta ruwaito hakan.

A yayin martani a madadin iyalan, Sarkin Ningi, Alhaji Yunusa Muhammad ya mika godiya ga gwamnan kan ta'aziyyarsa da addu'ar da yayi wa Hajiya Abu da iyalan ta.

Abba Ruma, Ministan Noma a zamanin 'YarAdu'a ya rasu a Landan

A wani labari na daban, Tsohon ministan noma da albarkatun ruwa, Dr Abba Sayyadi ruma ya riga mu gidan gaskiya. Leadership ta rahoto cewa Ruma ya rasu ne a wani asibiti a birnin Landan.

Kara karanta wannan

Cika shekaru 15 kan mulki: Takaitaccen tarihin Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar

Kawunsa kuma Danwairen Katsina, Alhaji Sada Salisu ya tabbatar da rasuwarsa tsohon ministan.

A cewar Sada, marigayin ya yi fama da ciwon sukari na tsawon lokaci kafin rasuwarsa, rahoton Daily Trust. Ya rasu ya na da shekaru 59 sannan ya bar mata 2 da yara 9.

An haife shi a ranar 13 ga watan Maris na 1962, marigayi Ruma minista ne wanda ya yi aiki tukuru a lokacin mulkin marigayi shugaban kasa Umaru Musa Yar’Adua.

Ruma ya rike kujerar shugaban hedkwatar kungiyar tattalin kudi don habaka harkar noma a Rome, kasar Italiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: