Zaben Anambra: Yan bindiga sun sace akwatunan zabe a rumfunar zabe

Zaben Anambra: Yan bindiga sun sace akwatunan zabe a rumfunar zabe

  • Wasu yan bindiga sun farmaki rumfunar zabe na Immaculate Heart Catholic Church da St Faith Catholic Church a Fegge, Onitsha
  • Maharan sun sace akwatunan zabe guda biyu na zaben gwamnan Anambra da ke gudana a yau Asabar, 6 ga watan Nuwamba
  • Da isar su rumfunar zaben, sai yan bindigar suka fara harbi ba kakkautawa domin su tsorata masu zabe da jami'an tsaro

Jihar Anambra - Yan bindiga sun sace akwatunan zabe biyu a rumfunar zabe na Immaculate Heart Catholic Church da St Faith Catholic Church a Fegge, Onitsha, jihar Anambra.

Maharan kimanin su shida sun kai farmaki rumfar St Faith Catholic Church da ke Mbonu Ejike/Basden Junction a cikin wata motar bas ta L300, rahoton The Nation.

Zaben Anambra: Yan bindiga sun sace akwatunan zabe a rumfunar zabe
Zaben Anambra: Yan bindiga sun sace akwatunan zabe a rumfunar zabe
Asali: UGC

Da isar su wajen sai suka fara harbi ba kakkautawa domin tsoratar da masu kada kuri’u da jami’an tsaro.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: An fara zabe a Awka da kewaye bayan an tsaurara matakan tsaro

Jaridar The Nation ta rahoto cewa kai tsaye yan bindigar suka tuka motarsu zuwa wajen akwatunan zaben sannan suka yi awon gaba da biyu daga ciki.

Wani shaida ya ce:

“Na tabbata akwatuna biyu ne a wajen amma wani jami’in INEC daga wajen da ya boye ya ce guda daya ne kawai.”

Daga masu kada kuri’u har Jami’an tsaro duk sun tarwatse daga cibiyar.

Wasu rukunin yan bindiga sun kuma farmaki rumfar zabe a Immaculate Heart Church da ke hanyar Ziks Avenue, inda suka sace akwatin zabe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng