Allah ya yiwa Farfesa Shehu Dalhatu na Jami'ar BUK rasuwa
- Babban Malami a Jami'ar Bayero dake Kano ya rigamu gidan gaskiya
- Farfesa Dalhatu ya rasu ne a kasar Masar inda yake jinya
- Ana shirin dawo da gawarsa Najeriya don jana'iza
Kano - Allah ya yiwa Farfesa Shehu Dalhatu na jami'ar Bayero dake Kano rasuwa da daren jiya, 5 ga watan Nuwamba, 2021 a kasar Masar bayan fama da rashin lafiya.
Farfesa Dalhatu gabanin rasuwarsa ya kasance Malami a tsangayar ilmin nazarin kimiyar siyasa a BUK.
Dan'uwan mamacin, Aminu Hayatu, ya sanar da mutuwar a shafinsa na Facebook, rahoton DailyTrust.
Farfesa yayi digirinsa na farko ne a Jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria a 1984 kuma yayi digirinsa na biyua Jami'ar a 1991.
Sai shekarar 2006 yayi digirinsa na uku Ph.D.
Mamacin ya kasance tsohon Shugaban kwalejin fasahar Kaduna Kadpoly.
A riwayar Solacebase, anan shirin dawo da gawarsa Najeriya.
Tsohon Malami a jami'ar Bayero BUK, AbdulRazak Gurnah, ya ci lambar yabon Nobel ta 2021
Marubuci dan asalin kasar Tanzania amma mazaunin kasar Birtaniya wanda ya karantar a jami'ar Bayero dake Kano ya ci kyautar lambar yabon Nobel na Adabi wannan shekarar.
Kwamitin zaben wadanda suka cancanci kyautar Nobel ta bayyana cewa an zabi Abdulrazak Gurnah ne bisa gudunmuwar da ya bada wajen rubuce-rubuce kan illolin mulkin mallaka da rayuwar yan gudun Hijra.
Asali: Legit.ng