Tsohon Malami a jami'ar Bayero BUK, AbdulRazak Gurnah, ya ci lambar yabon Nobel ta 2021

Tsohon Malami a jami'ar Bayero BUK, AbdulRazak Gurnah, ya ci lambar yabon Nobel ta 2021

  • Kwamitin bada kyautar Nobel ta zabi AbdulRazaq Gurnah bana
  • Gurnah ya karantar a Najeriya kafin komawarsa kasar Ingila
  • A baya Farfesa Wole Soyinka na Najeriya ya samu irin wannan kyautar

Sweden - Marubuci dan asalin kasar Tanzania amma mazaunin kasar Birtaniya wanda ya karantar a jami'ar Bayero dake Kano ya ci kyautar lambar yabon Nobel na Adabi wannan shekarar.

Kwamitin zaben wadanda suka cancanci kyautar Nobel ta bayyana cewa an zabi Abdulrazak Gurnah ne bisa gudunmuwar da ya bada wajen rubuce-rubuce kan illolin mulkin mallaka da rayuwar yan gudun Hijra.

A jawabin da Shugaban kwamitin Nobel Anders Olsson, ya saki ranar Alhamis a Shafin Nobel Prize na Facebook, ya bayyana cewa:

"An bada kyautar lambar yabon Nobel ta 2021 ga marubuci Abdulrazak Gurnah, wanda aka haifa a Zanzibar kuma mazaunin Ingila, bisa rashin gajiyawarsa da rubuce-rubuce kan illolin mulkin mallaka da rayuwar yan gudun Hijra a kasashe."

Read also

Sarkin Musulmi Da Shugaban CAN Sun Buƙaci a Kama Musulmin Da Suka Kashe Fasto a Kano

"Gurnah ya wallafa littatafai goma da kuma gajerun labarai barkatai."

Tsohon Malami a jami'ar Bayero BUK, AbdulRazak Gurnah, ya ci lambar yabon Nobel ta 2021
Tsohon Malami a jami'ar Bayero BUK, AbdulRazak Gurnah, ya ci lambar yabon Nobel ta 2021 Hoto: The Nobel Prize
Source: Facebook

Ya karantar a Jami'ar BUK

A cewar Wikipedia, Gurnah ya karantar a Jami'ar Bayero dake Kano tsakanin 1980 da 1982. Sannan ya koma Jami'ar Kent inda yayi karatun Doktoransa.

Yanzu ya zama Farfesa kuma shine Diraktan sashen digiri na biyu da uku a tsangayar yaren Turanci.

Source: Legit

Online view pixel