Yanzu-yanzu: Ana gab da fara zabe, Sifeto Janar ya canza kwamandan rundunar tsaro, DIG Egbunike
- A Oktoba, an tura DIG Joseph Egbunike jihar Anambra a matsayin babban jami'in dan sandan da zai jagoranci rundunar tsaro a zaben yau Asabar
- Amma ana saura yan sa'ao'i a fara zabe, Sifeto Janar na yan sanda, IGP Alkali Usman, ya sauya Egbunike
- Hukumar yan sanda dai bata bayyana dalilin da ya sa ta dau wannan mataki ba har yanzu
Sifeto Janar na yan sanda, IGP Alkali Usman, ya cire DIG Joseph Egbunike a matsayin kwamandan tsaro a zaben jihar Anambra da zai gudana ranar Asabar, 6 ga Nuwamba, 2021.
An cire DIG Joseph Egbunike ne ana saura yan awanni jama'a su fara kada kuri'a a jihar.
Kakakin hukumar yan sanda, CP Frank Mba, ya tabbatar da cire DIG Egbunike, amma bai bayyana dalilin da ya sa aka cire babban jami'in dan sandan ba.
Kakakin yan sandan yankin kudu maso gabas kuwa, Princess Nkeiruka Nwode, ta yi watsi da rahotanin cewa Egbunike ne yayi murabus da kansa, ta ce an tura shi wani aikin daban mai muhimmanci.
Ta kara da cewa wanan sauyi da akayi ba zai shafi zaben ba ko kadan.
Legit.ng ta tattaro cewa tuni an maye gurbin DIG Egbunike da DIG Zaki Ahmed, wanda shine mukaddashin jami'in gudanar da lamuran yan sanda.
Zaben Anambra: Babu abinci, dan sanda ya koka kan yunwar da ta addabe shi
A daidai lokacin da ake gudanar da zaben gwamnan jihar Anambra, wani jami'in dan sanda ya koka kan yunwar da ta addabe shi
Jami'in wanda ke tallafawa jami'an zabe wajen gudanar da aikinsu, ya yi korafin cewa ba a yi masu tanadin abincin da za su ci ba
Kimanin jami'an yan sanda sama da 30,000 aka tura jihar domin zaben wanda ke gudana a a yau Asabar, 6 ga watan Nuwamba
Asali: Legit.ng