Gwamna El-Rufai ya dauko Farfesa daga Ingila, ya nada shi a matsayin Mai bada shawara

Gwamna El-Rufai ya dauko Farfesa daga Ingila, ya nada shi a matsayin Mai bada shawara

  • Farfesa Rajneesh Narula ya zama Mai ba Gwamnatin Kaduna shawara a kan harkar kasafi da tattali.
  • Rajneesh Narula mai koyarwa a jami’ar Reading, yana cikin manyan masanan da ake ji da su a Duniya.
  • Masanin ya yi digirin farko a jami’ar ABU Zaria, daga nan ya saki-layi ya koma harkar tattalin arziki.

Kaduna - Gwamnatin jihar Kaduna ta bada sanarwar nada Farfesa Rajneesh Narula a matsayin mai bada shawara a hukumar tsare-tsare da kasafin kudi.

Jaridar The Cable ta bayyana cewa Rajneesh Narula zai taimakawa Gamnatin Kaduna wajen bada shawara a kan yadda za a dabbaka dabarun kasafin kudi.

Farfesa Narula zai bada gudumuwa wajen ganin tsare-tsaren gwamnatin ya kai ga kananan hukumomi ta karkashin majalisar tsare-tsaren tattalin.

Mai magana da yawun bakin gwamna Nasir El-Rufai, watau Muyiwa Adekeye ya bada wannan sanarwar a ranar Juma’a, 5 ga watan Nuwamba, 2021.

Kara karanta wannan

Matashi dan shekara 36 daga arewa yana neman 'kujera ta daya' a APC

Kamar yadda Dateline ta kawo rahoto, Muyiwa Adekeye ne mai taimakawa gwamnan jihar Kaduna wajen harkokin yada labarai da kuma sadarwa.

Rajneesh Narul
Farfesa Rajneesh Narul Hoto: www.henley.ac.uk
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wanene Farfesa Rajneesh Narula?

Rajneesh Narula ne shugaban cibiyar kula da harkokin kasuwanci na kasashen Duniya a jami’ar Reading kuma darektan cibiyar Dunning a Afrika ta kudu.

Kamar dai gwamnan Kaduna, Rajneesh Narula ya sakandare a Barewa College, sannan ya yi digiri a fannin fasaha a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

Bayan nan sai masanin ya samu digirgir na MBA da digirin PhD a jami’ar Rutgers a kasar Amurka.

Kafin ya bar Najeriya, Rajneesh Narula ya yi aiki a makarantar koyar da tukin jirgi ta NCAT da ke Zariya. Daga nan kuma ya koma aiki da IBM a Hong Kong.

Narula ya kware a kwadaito hannun jari da kawo cigaban tattalin arziki ta hanyar masana’antu, yana cikin wadanda suke fi kowa yawan rubuce-rubuce.

Kara karanta wannan

Shugaban CAN: Farashin kuɗin fansa ya ƙaru a Kaduna sakamakon rufe hanyoyin sadarwa da gwamnati ta yi

Sabon mai ba gwamnatin Kadunan shawara ya yi aiki da kungiyoyi a kasashen waje ECOWAS, UNIDO, UNCTAD, OECD, da kuma babban bankin Duniya.

Canji a gwamnatin Kaduna

Kwanakin baya kun ji Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi karin haske a kan alakarsa da Muhammadu Sanusi II da sauke Muhammad Sani Abdullahi.

Muhammad Sani Abdullahi shi ne tsohon shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin Kaduna, yanzu ya koma kan tsohuwar kujerarsa na kwamishinan kasafin kudi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng