Majalisa ta taso Ministan Buhari a gaba kan kwangilar jirgin kasa zuwa Jamhuriyar Nijar

Majalisa ta taso Ministan Buhari a gaba kan kwangilar jirgin kasa zuwa Jamhuriyar Nijar

  • Ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya gabatar da kasafin ma’aikatarsa na shekarar 2022 a Majalisa
  • ‘Yan majalisan sun soki yadda Najeriya take kashe kudi wajen aikin dogo zuwa Jamhuriyar Nijar.
  • Amaechi yace aikin zai taimakawa yammacin Afrika, kuma ya fadi wasu titunan jirgin da za ayi.

Abuja - Kwamitin majalisar dattawa da majalisar wakilan tarayya sun soki yunkurin gina titin jirgin kasa daga Kano zuwa garin Maradi a jamhuriyar Nijar.

Jaridar Punch tace kwamitin hadaka na sufurin kasa da na ruwa a majalisar tarayya sun koka kan yadda za a gina bari biyu a dogon da zai fita daga kasar.

A lokacin da sauran titunan jirgin kasa da ke Najeriya suke da bari daya, wannan dogo da za a gina daga Kano zuwa Maradi zai zo ne da barin hanya biyu.

Read also

Mangal zai bi sahun Dangote da BUA, zai gina sabon kamfanin Siminti a Najeriya

‘Yan majalisar sun fusata a lokacin da Ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya gabatar da abin da kasafin kudin shekara 2022 na ma’aikatarsa ya kunsa a jiya.

Ministan sufurin ya bayyana amfanin wannan gagarumin aiki, yace zai bunkasa kasuwanci a Afrika a lokacin da ake kukan an yi watsi da kudancin kasar.

Rotimi Amaechi
Ministan sufuri, Rotimi Amaechi Hoto: dailytrust.com

Amfanin gina titin jirgi zuwa Maradi

“Gina titin jirgin kasan Najeriya zuwa Maradi (kasar Nijar) mai kilomita 284 zai taimaka wajen saukaka kasuwanci tsakanin kasashen yammacin Afrika.”
“Wannan gudumuwa da Najeriyaa za ta bada zai taimakawa dukkanin kasashen ta hanyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Nijar da Najeriya.” – Amaechi.

Shugabannin kwamitocin Sanata Danjuma Goje da Honarabul Pat Asadu sun ce ana kyale sauran bangarorin kasa a wajen ayyukan gina hanyoyin jirgin kasa.

Da yake bayani a ranar Alhamis, 4 ga watan Nuwamba, 2021, Rotimi Amaechi ya bayyana cewa an soma yin aikin gina titin jirgi daga garin Abuja zuwa Kaduna.

Read also

Malaman addini sun fi shugabannin siyasa hatsari a halin yanzu, Aisha Yesufu

“An fara aikin gina titin jirgin kasa daga babban birnin tarayya Abuja zuwa garin Kaduna. An fara zanen titin jirgin kasan Ibadan-Minna-Abuja.” – Amaechi.

Asiri ya fara tonuwa a Zamfara

Gwamnan Zamfara Bello Matawalle ya ce masu ba 'yan bindiga bayanai sun tona asirin wasu ƴan siyasa.

Kamar yadda aka fitar da rahoto dazu, Gwamnan yace wasu daga cikin masu kwarmatawa yan bindigan bayanai sun ce yan siyasa ne ke ɗaukan nauyin aikinsu.

Source: Legit.ng

Online view pixel