Gwamnatin tarayya ta kashe N538m wajen zubar da tsofaffin kudi guda1.51bn

Gwamnatin tarayya ta kashe N538m wajen zubar da tsofaffin kudi guda1.51bn

  • Babban bankin Najeriya CBN ya ce an cigaba da zubar da tsaffin takardun kudin Najeriya masu datti don tabbatar da cewa sabbi ke yawo a gari
  • Takardun Nairan da aka zubar sun hada da na N1000 zuwa N5, amma N500 ne kashi 38.2% na lalatattun kudaden
  • An zuba tsaffin kudaden cikin akwati 151,427 kuma aka zubar da su inda aka kashe N538.59 wajen yin hakan

Abuja - Babban bankin Najeriya CBN ya ce an yi watsi da takardun kudi bilyan 1.51 na kimanin N698,480 million a 2020.

Wannan na kunshe cikin rahoton shekarar 2020 da sashen ayyukan kudi ta tattara.

A Najeriya, bankin CBN na lalata takardun Nairan da sukayi datti kuma suka yage domin tabbatar da cewa sabbin suka fi yawa hannun mutane.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta kashe N58.61billion wajen buga takardun kudin Najeriya guda 2.581 bilyan

Wannan na kunshe cikin dokar kafa CBN 2007, sashe na 18(d).

CBN yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"A karshen Disamban 2020, an zubar da takardun kudi guda bilyan 1.51 (akwati 151,427) na kudi kimanin N698,480 million, sabanin takardu bilyan 1.57 (akwati 157,217) na kimanin kudi N814,437.60 million da aka zubar a 2019."

Bankin yace adadin akwatuna cike da lalatattun kudin da aka zubar a 2020 ya yi kasa da akwati 5,790 idan aka hada da wadanda aka zubar a 2019.

"Dalilin haka shine dokokin kulle na cutar Korona," Bankin ya kara.

Nawa aka kashe wajen zubar da kudaden?

CBN ya bayyana cewa an kashe N538.59 million wajen zubar da wannan kudi a 2020, sabanin N647.82 million da aka kashe a 2019.

Gwamnatin tarayya ta kashe N538m wajen zubar da tsofaffin kudi guda1.51bn
Gwamnatin tarayya ta kashe N538m wajen zubar da tsofaffin kudi guda1.51bn
Asali: Twitter

Gwamnatin tarayya ta kashe N58.61billion wajen buga takardun kudin Najeriya guda 2.581 bilyan

Kara karanta wannan

Hoton karshe na ginin da ya rubto a Legas: Abubuwa 8 da ya kamata ku sani game da wannan gini

Babban bankin Najeriya CBN ya bayyana yadda aka kashe N58.618 billion wajen buga kudade guda 2.518 billion a shekarar 2020.

CBN ya bayyana hakan a rahoton da ya saki a shafinsa na yanar gizo.

A cewar rahoton. adadin da aka kashe a 2020, ya yi kasa da wanda aka kashe a shekarun 2019 da 2018.

A 2018, an kashe N64bn yayinda aka kashe N75bn a 2019.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng