Anambra: IGP ya takaita zirga-zirgar ababen hawa daga daren Juma'a gabanin zaben gwamna a ranar Asabar

Anambra: IGP ya takaita zirga-zirgar ababen hawa daga daren Juma'a gabanin zaben gwamna a ranar Asabar

  • A yayin da ake shirin zaben gwamnan Anambra, Sufeto Janar na yan sanda, Usman Baba, ya yi umurnin takaita zirga-zirgar ababen hawa a jihar
  • Dokar za ta fara aiki ne daga karfe 11:59 na daren ranar Juma'a, 5 ga watan Nuwamba zuwa karfe 11:59 na daren ranar Asabar
  • Hakan na daga cikin matakan kare martabar tsarin zaben wanda za a yi a ranar Asabar, 6 ga watan Nuwamba

Jihar Anambra - Gabannin zaben gwamna da za a yi a Anambra a ranar Asabar, 6 ga watan Nuwamba, Sufeto Janar na yan sanda, Usman Baba, ya yi umurnin takaita zirga-zirgar ababen hawa a jihar.

Dokar za ta fara aiki daga karfe 11:59 na daren ranar Juma'a, 5 ga watan Nuwamba zuwa karfe 11:59 na daren ranar Asabar, jaridar Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban kamfanin dillancin labaran Najeriya, Jide Adebayo, ya mutu

Anambra: IGP ya takaita zirga-zirgar ababen hawa daga daren Juma'a gabanin zaben gwamna a ranar Asabar
Anambra: IGP ya takaita zirga-zirgar ababen hawa daga daren Juma'a gabanin zaben gwamna a ranar Asabar Hoto: Nigeria Police.
Asali: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, Frank Mba, ya saki a ranar Alhamis, mai taken: 'Zaben Anambra: IGP ya yi umurnin takarta zirga-zirgar ababen hawa', ruwayar PM News.

Sanarwar ta ce:

“A wani bangare na matakan kare martabar tsarin zaben gwamnan jihar Anambra a ranar 6 ga Nuwamba, 2021, Sufeto Janar na yan sanda, Usman Baba, ya yi umurnin takaita zirga-zirgar ababen hawa a ciki da wajen jihar Anambra daga 11:59PM a ranar Juma'a, 5 ga watan Nuwamba zuwa 11:59pm na ranar Asabar, 6 ga watan Nuwamba, 2021.
"IGP ya bayyana cewa akwai bukatar sanya dokar takaita zirga-zirgar sakamakon bincike na tsaro da ke nuna wasu miyagu na iya kutsawa jihar Anambra, kafin, lokaci da kuma bayan zaben."

Kara karanta wannan

Tituna sun yi wayam babu kowa yayin da mazauna Anambra suka fara zaman gida duk da soke umurnin da IPOB ta yi

IGP ya kuma bayyana cewa matakin zai ba rundunar tsaro damar lura da jihar sosai wajen tabbatar da tsaro domin dakile safarar ‘yan bangar siyasa da masu tada kayar baya, da kuma hana amfani da kananan makamai da miyagun kwayoyi a lokaci da bayan zaben.

Ya umurci jami’an zabe, masu sa ido da aka tantance, ‘yan jarida da sauran jami’an da aka ba izini da su gudanar da ayyukansu bisa doka a lokacin zaben tare da sanya katin shaidarsu.

Tituna sun yi wayam babu kowa yayin da mazauna Anambra suka fara zaman gida duk da soke umurnin da IPOB ta yi

A wani labarin, mun ji cewa, a yayin da ake shirye-shiryen zaben gwamnan jihar Anambra a gobe Asabar, 6 ga watan Nuwamba, yawancin unguwanni a jihar sun yi tsit babu kowa yayin da mazauna yankin suka shige gida saboda dokar zaman gida na sati guda.

Duk da cewar kungiyar awaren IPOB ta soke umurnin a yammacin ranar Alhamis, 4 ga watan Nuwamba, mazauna jihar sun ki fitowa saboda tsoron kada a far masu ko kuma a ci zarafin su.

Kara karanta wannan

Zaben Anambra: Bayani a kan ‘Dan takarar APC wanda ya taba yin Gwamna na kwana 17

Wakilin Legit.ng wanda ya ziyarci wurare da dama dake da yawan hada-hada a babban birnin jihar kamar Unizik Junction, Ifite, Okpuno Agu Awka ya lura cewa harkokin kasuwanci sun tsaya cak a yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng