Ba tare da bayyana dalili ba, Dakarun soji sun fice sun bar yan sanda da aikin tsaro a wannan jihar

Ba tare da bayyana dalili ba, Dakarun soji sun fice sun bar yan sanda da aikin tsaro a wannan jihar

  • Jami'an rundunar soji sun janye daga madakatun bincike a jihar Ondo, kuma ba tare da bayyana dalili ba
  • Tuni hukumar yan sanda ta jibge jami'an ta a waɗan nan wuraren da sojoji suka tashi, domin cigaba da kare al'umma
  • Wannan lamari ya jawo musayar yawu tsakanin gwamnatin jihar da kuma babbar jam'iyyar hamayya PDP

Ondo - Dailytrust ta ruwaito cewa yanzun haka yan sanda sun maye gurbin wuraren bincike da sojoji ke kula da su a jihar Ondo.

Wannan dai ya zo ne biyo bayan janyewan da sojoji suka yi bisa wani dalili da har yanzun ba su fito sun bayyana ba.

Duk da cewa sojojin ba suce komai game da janyewar su ba, amma PDP ta yi zargin cewa gwamnan jihar, Oluwarotimi Akeredolu, shine baya biyan su alawus.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi ram da mijin da ya soka wa matarsa almakashi, ta sheka lahira

Jami'an soji
Ba tare da bayyana dalili ba, Dakarun soji sun fice sun bar yan sanda da aikin tsaro a wannan jihar Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Sai dai tun ba'a je ko ina ba, gwamnatin jihar Ondo ta fito ta musanta zargin da jam'iyyar PDP ta jefa mata.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Me gwamnatin jiha tace game da lamarin?

A wata sanarwa ɗauke da sa hannun kwamishinan yaɗa labarai, Mista Donald Ojogo, gwamnatin Ondo ta zargi PDP da saka siyasa a lamarin kare rayuwar al'umma da walwalar su.

Wani sashin sanarwan yace:

"Gwamnatin jihar Ondo ba zata tsaya cece-kuce ko wani dogon labari akan biyan alawus din jami'an tsaro ba, domin hukumar da abin ya shafa har yanzun ba ta fitar da jawabi ba."

Wane mataki yan sanda suka ɗauka bayan janyewan sojoji?

Kakakin yan sandan jihar, Funmi Odunlami, tace tuni aka tura jami'ai zuwa wuraren dake faɗin jihar domin ɗorawa daga inda aka tsaya.

Tace:

"Bayan abinda ya faru, mun tura jami'an mu zuwa wuraren da abun ya shafa, saboda mutane na tsoron za'a iya samun matsala a kowane lokaci. Dan haka muka ɗauki mataki tun da wuri."

Kara karanta wannan

Aƙalla mutum 7 suka mutu yayin da miyagun yan bindiga suka kai harin farko yankin wannan jihar

Daga nan kuma ta roki direbobi da yan acaba su cigaba harkokinsu kamar yadda suka saba, kuma su kai rahoton duk wani abu da ɗan sanda ya yi ba dai-dai ba.

An sace mata zalla a Neja

A wani labarin na daban kuma Hukumar yan sanda reshen jihar Neja ta bayyana cewa wasu yan bindiga sun yi awon gaba da mata huɗu a yankin karamar hukumar Suleja

Kwamishinan yan sandan jihar, Monday Kuryas, yace maharan sun farmaki kauyen ne da tsakar daren Laraba.

Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa yan bindigan sun buɗe wuta da zuwansu domin tsorata mutanen ƙauyen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262