Jang da gwamnatin Plateau an yi "uwar watsi" kan tsige kakakin majalisa
- Tsohon gwamnan Filato, Jonah David Jang ya caccaki gwamnatin jihar kan tsige kakakin majalisa Nuhu Abok Ayuba
- Jang ya zargi gwamnan da kulla makarkashiya wacce 'yan majalisar suka aiwatar tare da tsige Abok Ayuba daga mukaminsa
- Tsohon gwamnan ya yi kira ga dattawan jihar da su saka baki tare da kawo karshen wannan rigimar gudun abinda zai je ya dawo
Filato - Tsohon gwamnan jihar Filato, Jonah David Jang da gwamnatin jihar Filato suna sukar juna tare da cacar baki kan tsige kakakin majalisar, Nuhu Abok Ayuba da aka yi a makon da ya gabata.
'Yan majalisa 16 daga cikin 24 sun amince da tsige Abok tare da maye gurbinsa da Yakubu Sanda, amma kuma lamarin ya cigaba da janyo cece-kuce, Daily Trust ta wallafa.
A yayin tsokaci kan tsigewar a wata takarda da ya fitar, Jang ya yi kira ga dattawan Filato da su shigo cikin rikicin shugabancin da ya mamaye majalisar jihar domin a guje wa bin son ran kadan daga cikin 'yan majalisar wurin muzgunawa jama'ar jihar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Daily Trust ta ruwaito cewa, tsohon gwamnan wanda ya ce zai jagoranci masu zanga-zanga domin a dawo da tsigaggen kakakin, ya yi kira ga dattawan da su tashi tsaye kan gwamnan jihar, Simon Lalong, domin dawo da zaman lafiyan gidan.
Ya kara da yin bayanin cewa, duk da kokarin da Gwamna Lalong yayi na nisanta kansa daga abinda ke faruwa a majalisar jihar, a bayyane ya ke cewa wadanda suka tabbatar da tsige kakakin sun bi umarnin gwamnan ne.
A cewar Jang:
"Tabbas mu ganau ne a abinda ya faru da kuma rikicin da ya hadiye majalisar jihar saboda wani bangaren na gwamnatin na son ganin bayan kakakin majalisar ta kowanne hali.
"Yayin da abinda ya faru ya zama abun takaici yanda wadansu mutane suka saka son ransu tare da yin duk abinda zai kawo jin kunya, ba za mu kalmashe hannuwan mu ba wurin tabbatar da an dawo da zaman lafiyan jihar".
“Saurin da gwamna yayi wurin karbar sabon kakakin majalisar, wanda kuma a matsayinsa na lauya, ya bayyana abubuwa masu tarin yawa.
“Shaidu sun nuna cewa, yawan mutanen da ake bukata domin tsige mutum babu su, hakan yasa suka yi amfani da karfi wurin aiwatar da mummunan nufinsu," ya kara da cewa
Ba zan yarda ba, Kakakin majalisar dokokin Plateau da aka tsige ya bude nasa majalisar
A wani labari na daban, rikici ya barke a majalisar dokokin jihar Plateau, Kakakin da aka tsige ya ce ba zai yarda ba.
Tsigaggen Kakakin majalisar Nuhu Abok, ya bude nasa zauren majalisar a wajen majalisa yan sa'o'i bayan tsigeshi da aka yi, rahoton TVC News.
Ba tare da bata lokaci, ya shirya zama tare da wasu a waje da wadanda ke goyon bayansa.
Asali: Legit.ng