Da Dumi-Dumi: Rikici ya barke tsakanin yan Keke-Napep da jami'an yan sanda, An bindige mutum daya
- Direbobin Keke-Napep sun mamaye kan hanya domin nuna fushinsu kan kisan da wani ɗan sanda ya yi wa ɗayansu a jihar Legas
- Rahotanni sun bayyana cewa sun fara wannan zanga-zanga ne bayan bindige ɗan Napep ɗaya har Lahira a bakin titi a yankin Meran
- Kwamishinan yan sandan jihar, Hakeem Odumosu, ya tura jami'an sintiri zuwa yankin domin dawo da zaman lafiya
Lagos - Yanzun haka direbobin Keke-Napep na can suna zanga-zanga a yankin Abule-Egba dake jihar Legas bisa zargin jami'an yan sanda da harbe ɗaya daga cikinsu.
Dailytrust tace direbobin Napep sun mamaye hanyoyi da safiyar Alhamis, inda suka toshe hanyar shiga da fita Anguwan Meran, wani yanki a Abule-Egba.
Masu zanga-zangar sun ɗauki wannan matakin ne domin nuna fushinsu kan yadda jami'an yan sanda ke cin mutuncinsu har takai ga harbi.
Meya faru aka kashe ɗan Napep?
Wasu na zargin cewa jami'in hukumar yan sanda ne ya daba wa direban Keke-Napep ɗin wuka yayin da wasu ke cewa bindige shi ya yi, kuma ya barshi nan kan hanya har ya mutu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Rahotanni sun bayyana cewa rikicin dai tsakanin yan sanda da direbobin Napep ɗin ya faru ne a kan hanyar Command, Meran, Abule-Egba, ranar Alhamis.
Wane mataki hukumar yan sanda ta ɗauka?
Kakakin hukumar yan sanda rashen jihar Legas, Adekunle Ajisebutu, ya tabbatar da faruwar lamarin ta saƙon WhatsApp.
Ya kuma ƙara da cewa kwamishinan yan sanda na jihar Legas, Hakeem Odumosu, ya tura ƙarin jami'an yan sanda wurin domin kwantar da tarzomar.
Punch ta rahoto kakakin yan sandan yace:
"Kwamishinan yan sanda ya tura ƙarin jami'an sintiri zuwa yankin domin dawo da zaman lafiya da doka da oda."
A wani labarin kuma mun kawo muku Yadda wata yar bautar kasa NYSC ta mutu a Legas bayan ta guje wa matsalar tsaro a Borno
Mahaifiyar Zaynab Sanni Oyindamola, wata mambar NYSC ta samar wa ɗiyarta canjin wurin aiki daga jihar Borno saboda rashin tsaro.
Hakanan kuma mahaifiyar tana son ɗiyarta ta yi aiki a wuri mai tsaro kuma wanda bata sani ba, amma ashe hakan wata ƙaddara ce take kiranta.
Asali: Legit.ng