KAI TSAYE: Saura kwana 2 zaben Anambra, yan takara sun taru a daki daya don tabbatar da babu rikici
Komai ya kankama wa dukkan yan takara a zaben Gwamnan jihar Anambra, sun rattafa hannu kan takardar tabbatar da an yi zaben ranar 6 ga Nuwamba cikin zaman lafiya.
Wannan taro na gudana ne a Cibiyar tunawa da Dora Akunyili dake Awka, jihar Anambra.
Kwamitin zaman lafiya ta Najeriya NOC karkashin jagorancin Janar Abdusalami Abubakar (Rtd)
Wakilin Legit.ng na taron kuma zamu kawo muku bayanai kai tsaye.
Yan takara da masu ruwa da tsaki sun dauki hoto
Yan takara a zaben, Janar Abdis Sallam Abubakar, Fada Mattew Kukah, DIG Egbunike da sauransu sun dauki hoto
Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu, ya rattafa hannu
Dan takarar jam'iyyar PDP, Valentine Ozigbo, ya rattafa
Dan takaran jam'iyyyar APC ya rattafa hannu
An kaddamar da rattafa hannu kan takardar yarjejeniya tsakanin yan takara
An fara rattafa hannu kan takardar yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin yan takara.
Dan takaran jam'iyyar Accord, Maduka Godwin, ne zai fara rattafa hannu.
Mambobin kwamitin diflomasiyya sun dira wajen
Dan takaran jam'iyyar APC, Andu Uba ya dira wajen
Shugaban hukumar INEC, Prof Mahmud Yakubu, ya dira wajen
Janar Abdus Salam Abubakar da Fada Kukah sun dira wajen
Mambobin Kwamiti zaman lafiya Janar Abdus Salam Abubakar da Rev Fr. Kukah sun dira wajen taron.
Dan takaran jam'iyyar ZLP, Obiora Okonkwo ya dira wajen
Charles Soludo ya dira taron
Dan takaran jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) Professor Chukwuma Soludo, ya dira taron.
An fara rijistan mahalarta
An fara rijistan mahalarta taro, mambobin kungiyoyin fafutuka, yan jarida, jam'iyyun siyasa, da yan siyasa.