Kano: 'Yan sintiri sun yi ram da mutumin da ke bayyana wa mata al'aurarsa
- 'Yan sintiri sun yi ram da Sani Saleh a yankin Medile da ke jihar Kano kan zargin bayyana al'aurarsa a cikin jama'a
- Mataimakin kwamandan 'yan sintirin ya ce Saleh ya na fito da al'aurarsa ne ga mata kadai kuma ya tsere kafin zuwan maza
- An samu korafi daga mata masu tarin yawa kuma an kama shi ne bayan ya hantari wasu gungun yara mata a yankin
Kano - Wata kungiyar 'yan sintiri a jihar Kano ta yi ram da wani mutum mai suna Sani Saleh wanda ake zarginsa da bayyana al'aurarsa a cikin jama'a.
Salisu Idris, mataimakin kwamandan 'yan sintirin da ke yankin Medile a karamar hukumar Kumbotso ta jihar ya sanar BBC cewa wanda ake zargin an dade ana nemansa bayan an samu korafi daga mata daban-daban kan aika-aikar da ya ke yi.
"A duk lokacin da ya ga kungiyar mata, kawai sai ya cire wandonsa. Kafin maza su bayyana a wurin, sai ya tsere," Idris yace.
"Daga bisani mun kama shi bayan ya hantari wasu gungun yara mata a ranar Litinin, 1 ga watan Nuwamba," ya kara da cewa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kano: Rayuka 5 sun salwanta, mutum 2 sun jigata a mummunan hatsarin mota
A wani labari na daban, rayuka biyar sun salwanta, wasu biyu sun samu miyagun raunika a mummunan hatsarin da aka yi wanda ya hada da wata mota kirar Volkswagen da adaidaita sahu kan titin Kwanar Dumawa zuwa Kunya a karamar hukumar Minjibir ta jihar Kano.
Mummunan hatsarin da ya auku a ranar Talata, ya ritsa da fasinjojin da ke kan hanyarsu ta zuwa kauyukan da ke kusa da wurin, Daily Trust ta wallafa.
A yayin tabbatar da aukuwar lamarin, kwamandan hukumar kula da hadurra na yankin, Zubairu Mato, ya ce hatsarin ya auku ne sakamakon tsabar gudun ababen hawan.
Ya ce rayuka biyar da suka hada da maza hudu da mace daya sun rasa rayukansu yayin da wasu maza biyu suka samu miyagun raunika, Daily Trust ta wallafa.
Kamar yadda yace, bayan samun rahoton hatsarin, tawagarsa da ke ofishin Minjibir sun isa wurin kuma sun kwashe mutanen zuwa manyan asibitocin Minjibir da Danbatta inda likitoci suka tabbatar da mutuwar biyar daga ciki.
Asali: Legit.ng