Bamu yarda da su ba: Amotekun ta kama wasu ƴan arewa 18 cikin trelar wake a Ogun, ta ce su koma inda suka fito
- Jami’an tsaron Amotekun sun kama ‘yan arewa 18 bayan haduwa da tirelar waken da su ka boye a cikin ta tun daga arewacin Najeriya zuwa jihar Ondo a daidai kan titin Arakale da ke babban birnin jihar
- Kwamandan rundunar, Cheif Adetunji Adeleye ne ya bayyana hakan, inda ya ce da jami’an su ba su ci karo da su ba, da yanzu sun tayar da tarzoma kuma an fara bincike a kan wasu 30 da su ka isa yankin kafin su
- Adeleye ya ce za su bincike su don jin abinda ya kawo su yankin sannan a mika su ga shugaban hausawan yankin don tabbatar da an mayar da su inda su ka fito
Jihar Ondo - Jami’an tsaron Amotekun sun kama wasu ‘yan arewa 18 bayan cin karo da tirelar da ta dakko su daga arewacin Najeriya zuwa jihar bisa ruwayar TVC News.
An kama su ne a kan titin Arakale da ke Akure, babban birnin jihar Ondo a wannan makon.
LIB ta bayyana yadda shugaban jami’an ya ce ‘yan arewan barazana ne ga tsaron yankin ganin yadda su ke ta kai komo a hedkwatar jami’an da ke Alagbaka a Akure ma abin zargi ne.
Kwamandan rundunar, Cheif Adetunji Adeleye ya bayyana hakan inda ya ce an fara cin karo da ‘yan arewan a babban titin Ilesa-Akure.
Kwamandan ya bayyana yadda su ka shiga garin ta hanyar boyewa a karkashin lodin waken da ke cikin tirelar.
A cewar sa:
“Jami’an mu sun ga tirelar waken wacce ta nufi Akure. Sun tsaya a daidai titin Akure, yayin da ake binciken motar ne aka gano cewa samari guda 18 ne ba wake ba.”
Ya ce akwai bukatar su sanar da abinda ya kawo su
Adeleye ya ce wajibi ne matasan su bayyana gaskiyar dalilin da ya sa su ka kwaso kafafun su daga jihohin su zuwa jihar.
Ya kara da cewa za a mika su ga shugaban hausawan yankin don mayar da su daga inda su ka fito. Adeleye ya ce za su iya tayar da tarzoma da ba a dakatar da su ba.
A cewar sa akwai wasu 30 da ake zargin sun riga sun isa garin, kuma za a binciko su don yanzu haka jami’an sun fara neman su.
Abin da yasa har yanzu Nigeria bata zama ƙasaitacciyar ƙasa ba, Ministan Buhari
A wani labarin daban, Ministan Kimiyya da Fasaha, Ogbonnaya Onu, ya ce har yanzu Nigeria bata cimma babban matakin da ake sa ran ta kai ba a lokacin samun 'yanci saboda an yi watsi da irin halayen mazajen jiya da suka kafa kasar.
Ya yi wannan jawabi ne a babban birnin tarayya Abuja wurin wani taro da kungiyar 'Yan Kabilar Igbo ta shirya don karrama Rear Admiral Godwin Kanu Ndubuisi (mai ritaya), Daily Trust ta ruwaito.
Onu ya ce ya zama dole 'yan Nigeria su zama masu gaskiya, aiki tukuru da riko da halaye na gari idan suna son ganin kasar ta zama tauraro tsakanin sauran kasashe.
Asali: Legit.ng