Yan bindigan da suka saci Malamai a Jami'ar Abuja (UniABuja) sun bukaci N300m kudin fansa
- Yan bindigan da suka kai hari rukunin gidajen Malaman jami'ar Abuja dake Gwagwalada sun tuntubi iyalansu
- Da farko mun ruwaito muku cewa an sako su, amma mutum biyu yan bindiga suka sake basu shiga daji da su ba
- 'Dan daya daga cikin wadanda aka sace yace sun bukaci N50m kan kowani mutum guda
Abuja - Yan bindigan da suka yi awon gaba da mutum shida a gidan Malaman jami'ar Abuja (UniAbuja) sun bukaci kudin fansa daga wajen iyalan wadanda suka sace.
Mai magana da yawun jami'ar, Habib Yakoob, ya bayyana hakan, TheCable ta ruwaito.
A cewarsa:
"Sun ce a basu N300 million. Ban sani ko sun bada adadin kwanakin ba tukun."
TheCable tace Mustapha Sambo, 'dan daya daga cikin wadanda aka sace ya laburta mata cewa yan bindigan da suka sace mahaifinsa sun bukaci N100 million.
A jawabinsa ga TheCable:
"Sun dauki wayoyinmu da wallet dinsa. Sun ce suna bukatar kudi. Da muka ce babu kudi a gida, sai suka tafi da shi kuma suka ce sai mun biya N100 million kafin su sakeshi."
Sun sako wasu, amma har yanzu akwai mutum 6 hannunsu
An samu labaran cewa wasu cikin wanda yan bindiga suka sace a Jami'ar birnin tarayya Abuja sun samu kubuta.
The Sun ta ruwaito wani ma'aikaci a jami'ar da ya tabbatar da maganar cewa an ganosu ne a garin Abaji, kan babban titin Abuja-Lokaja, bisa taimakon jami'an yan sanda da bijilanti.
Yanzu haka suna ofishin yan sandan Abaji.
Daga cikin wadanda aka sake akwai matar Farfesa Bassey da kuma dan Farfesa Obansa.
Asali: Legit.ng