Yan bindiga sun kashe Limamin Masallacin Juma'a da yaki yarda a tafi da shi, sun sace yaransa

Yan bindiga sun kashe Limamin Masallacin Juma'a da yaki yarda a tafi da shi, sun sace yaransa

  • Wasu yan ta'adda sun yi yunkurin awon gaba da Limamin gari guda amma yaki yarda su tafi da shi
  • Limamin na aiki a gona tare da wasu yara mata dake taya shi aikin lokacin da yan bindiga suka far masa
  • Sun hallaka dattijon kuma sun yi awon gaba da yara matan

Katsina - Tsagerun yan bindiga sun hallaka Babban Limamin Masallacin Juma'an Sabon Garin Bilbis dake jihar Katsina bayan kin yarda su yi awon gaba da shi cikin gona.

Limamin mai suna Malam Adam ya gamu da ajalinsa da safiyar Litinin a gonarsa dake wajen garin Faskari, rahoton Premium Times.

Sabon Garin Bilbis, wani gari ne dake karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina, kuma mai iyaka da jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Bincika Gaskiya: Shin hukumar 'yan sanda ta dawo da Abba Kyari bakin aiki bayan bincike?

Yan bindiga sun kashe Limamin Masallaci
Yan bindiga sun kashe Limamin Masallacin Juma'a da yaki yarda ayi a tafi da shi, sun sace yaransa Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

Wani mamban kwamitin Masallacin, Lawal Mamman, wanda ya sanar da mutuwar Limamin ya bayyana cewa yan bindigan sun kwashe yara mata dake aiki tare da Malamin lokacin da suka kai harin.

A cewarsa, yan bindigan sun umurci Limamin ya bi su kan babur amma yace ba zai yi ba.

A cewarsa:

"Sun fara yi masa barazana da bindiga amma yace babu inda za shi duk da cewa sun ce zasu kashe shi."
"Ya fada musu cewa yana da matsala a kafa kuma ba zai iya binsu cikin daji ba."
"Bayan mujadalan, daya daga cikin yan bindigan yace kawai su kashe shi su bar wajen. Haka kuma suka kashe shi suka tafi da matan."

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng