Da Dumi-Duminsa: Wani gini mai hawa-hawa ya sake kifewa a jihar Legas
- Rahoto daga jihar Legas ya bayyana cewa wani gini mai hawa-hawa ya kife awanni 24 bayan mai hawa sama da 20 ya ruguje
- Lamarin dai ya faru ne da safiyar Talata, kuma ginin ya rushe ne bayan wani mamakon ruwa da aka yi da dare
- Jami'ai hukumar bada agaji, NEMA, da sauran hukumomi na cigaba da aikin ceto a wurin gini mai hawa sama da 20
Lagos - Wani gini mai hawa biyu ya ruguje a yankin Anguwar Lekki dake jihar Legas, ranar Talata, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Rahoto ya bayyana cewa ginin wanda ba'a kammala shi ba, ya rushe ne bayan a yi wani mamakon ruwa ranar Litinin da daddare.
Wannam na zuwa ne awanni 24 bayan dogon gini mai hawa sama da 20 ya rushe a yankin Ikoyi, na jihar ta Legas.
Halin da ake ciki wajen ceto mutane?
Jami'an hukumar agaji NEMA sun samu nasarar gano gawar mutum uku daga cikin dogon ginin da ya rushe a jihar Legas.
Hakanan an kuma ceto wasu mutunw da suke da sauran numfashi a gaba, suna asibiti ana kulawa da lafiyarsu.
Babban ginin, wanda ake cikin ginawa, ya ruguje ne a kan hanyar Gerald dake yankin Anguwar highbrow a jihar Legas.
Shugaban hukumar bada agajin gaggawa, NEMA, Ibrahim Farinloye, yace an matsar da gawarwakin zuwa ɗakin ajiye gawa mallakin gwamnatin jihar Leagas.
A wani labarin na daban kuma Bayan harin masallaci, yan Bijilanti sun kashe mutum 9, sun ƙona gidaje a wata rugar Fulani a jihar Neja
Rahoto ya nuna cewa maharan sun ƙone gidaje a wata rugar Fulani, bayan kashe dagacin Adogon Mallam da ɗan uwansa.
Hukumar yan sanda ta tura jami'anta na musamman domin kame duk wani mai hannu a harin.
Asali: Legit.ng