Shugabannin addinai suna amfana daga mulkin zalunci a Najeriya, Inji Aisha Yesufu

Shugabannin addinai suna amfana daga mulkin zalunci a Najeriya, Inji Aisha Yesufu

  • Aisha Yesufu ta sake caccakar malaman addinai baki ɗaya da cewa suna amfana da rashin jagoranci mai kyau
  • Shahararriyar yar fafutukar tace shugabannin addinai a Najeriya suna amfana wajen cinikin kayayyakin su na mu'ujiza da wahayi
  • Aisha ta yi ƙaurin suna a lokacin zanga-zangar EndSARS da ta gudana a shekarar da ta gabata 2020

Lagos - Shahararriyar yar fafutukan nan, Aisha Yesufu, ta bayyana cewa shugabannin addinai suna amfana daga shugabanci mara kyau.

Jaridar Punch ta ruwaito yar fafutukar na cewa rashin kyakkyawan shugabanci yana taimaka wa malamai wajen cinikin kayan al'ajabi da kuma karfin magana.

Ta faɗi haka ne yayin da take martani kan maganar shugaban Deeper Christian Life Ministry, William Kumuyi, wanda ya gargaɗi kiristoci su daina zagin shugabanni.

Kara karanta wannan

Ka daina zagin Buhari ka biya albashi da fansho: 'Yan Benue sun caccaki gwamnansu

Aisha Yesufu
Shugabannin addinai suna amfana daga mulkin zalunci a Najeriya, Inji Aisha Yesufu Hoto: @Aisha Yesufu
Asali: Facebook

Me malamin ya faɗa?

Kumuyi ya kuma yi magana kan rashin kyaun shiga duk wani abu da zai jawo lalata kayayyaki da dukiyoyin mutane da na gwamnati saboda gaza cika alƙawarurran yan siyasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Faston yace:

"Mun koyar daku matukar kana da cikakken imanin kiristanci to ba zaka tsani makocinka ba."
"Hakanan ba zaka je kana lalata kayayyakin gwamnati ba saboda kawai waɗan da ke kan madafun Iko sun gaza cika alƙawarin da suka ɗauka."
"Mun koyar da rayuwa mai kyau a addinin mu na kirista, ba zai yuwu ka zama mai bin Allah ranar Lahadi kuma ka zama mai cutar wa ranar Litinin ba."

Martanin Aisha Yesufu

Guardian ta ruwaito Aisha Yesufu tace:

"Shugabannin addinai sun fi hatsari a kan shugabannin siyasa, sun maida mabiyansu tamkar bayi, kuma suna son shugabanci mara kyau domin cinikin mu'ujizar su."

Kara karanta wannan

A yi wa yan bindiga Afuwa kuma a ware kuɗaɗen ɗaukar nauyinsu, Sheikh Gumi ya magantu

"Har zuwa lokacin da zasu bar mutane su huta da kamannin Malamai, Fastoci, dibias, babalawos da boka, ba abinda zai canza."

A wani labarin kuma Wata Budurwa ta mutu jim kadan bayan ta kwana a dakin saurayinta

Wata dalibar kwalejin fasaha a jihar Osun ta mutu jim kaɗan bayan dawowa daga ɗakin saurayinta inda da takai masa ziyara.

Rahoto ya nuna cewa ɗalibar mai suna Wumi, ta kamu da rashin lafiya ne bayan ziyarar ɗakin, ta mutu akan hanyar zuwa Asibiti.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262