Tashin Hankali: Wata Budurwa ta mutu jim kadan bayan ta kwana a dakin saurayinta

Tashin Hankali: Wata Budurwa ta mutu jim kadan bayan ta kwana a dakin saurayinta

  • Wata dalibar kwalejin fasaha a jihar Osun ta mutu jim kaɗan bayan dawowa daga ɗakin saurayinta inda da takai masa ziyara
  • Rahoto ya nuna cewa ɗalibar mai suna Wumi, ta kamu da rashin lafiya ne bayan ziyarar ɗakin, ta mutu akan hanyar zuwa Asibiti
  • A halin yanzun yan sanda sun yi awon gaba da matashin saurayin domin gudanar da bincike

Osun - Kwalejin fasaha ta jihar Osun ta bukaci a gudanar da bincike kan musabbabin mutuwar ɗaya daga cikin ɗalibanta mata mai suna Wumi.

Jaridar Punch tace ɗalibar, wacce take shekarar karatunta ta ɗaya a sashin koyon aikin jarida, ta mutu ne ranar Asabar, bayan gajeriyar rashin lafiya a ɗakin Saurayinta.

Rahotanmi sun bayyana cewa Wumi na fara nuna wasu alamu na rashin lafiya aka gaggauta kai ta asibiti mai zaman kansa a Iree, amma suka ƙi amsarta.

Kara karanta wannan

A yi wa yan bindiga Afuwa kuma a ware kuɗaɗen ɗaukar nauyinsu, Sheikh Gumi ya magantu

Kwalejin fasaha a jihar Osun
Tashin Hankali: Wata Budurwa ta mutu a dakin Saurayinta jim kadan bayan ta kai masa ziyara Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Ɗalibar ta ƙarasa mutuwa ne yayin da ake kokarin canza mata wani Asibitin na daban, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shin ana zargin saurayin nata?

Wata ɗaliba da suke karatun kwas ɗaya, wacce ta nemi a sakaya sunanta, ta bayyana cewa jami'ai sun damƙe saurayin da zargin hannu a mutuwarta.

Ɗalibar tace:

"Wumi ta ziyarci gidan saurayinta a yankin Igaa dake Iree, ba zato sai ta fara fitar da kumfa daga bakinta. Nan take akai gaggawar kaita Asibiti a Iree, amma suka ƙi amsarta, kafin a kaita wani kuma ta mutu."
"Ƙawayenta suka kai rahoto wurin yan sanda, nan take suka turo jami'ai, suka ɗauki gawarta zuwa ɗakin aje gawarwaki a Ikirun."
"Saurayin na ta shima ɗalibi ne a kwalejin, jami'an yan sanda sun damke shi, sun tafi da shi ofishin su.

Kara karanta wannan

Mafi munin mulkin soja da aka taba yi a Najeriya yafi gwamnatin Buhari walwala da jin daɗi, Ortom

Kwalejin ta tabbatar da mutuwar Wumi

Kakakin kwalejin, Tope Abiola, ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya bayyana cewa wanda ake zargi ba ɗalibin su bane.

Yace:

"Eh, dagaske ne ɗalibar ND 1 dake karatu a sashin jarida ta rasa rasuwarta, amma ba mu san musabbabin mutuwarta ba."
"Yan sanda na cigaba da bincike. Makaranta na yiwa iyayen ɗalibar ta'aziyyar mutuwarta, da zafi sosai matashiyar yarinya ta mutu ba zato ba tsammani."

A wani labarin kuma Ya kamata na sassauta mishi, Jaruma Mansurah Isa ta sake magana kan tsohon mijinta Sani Danja

Jaruma Mansurah Isah ta yi wani rubutu a kan tsohon mijinta, Sani Musa Danja, tare da sakin wasu sabbin hotunanta tare da shi.

Jarumar ta nuna cewa tana da kyakkyawar alaƙa tsakaninta da shi, kuma ta yi wasu kalamai na barkwanci akan Jarumin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: