An harbe mahalarta daurin aure a Afghanistan saboda sun saurari wake-wake
- Ana zargin ‘Yan Taliban da hallaka mutane a wajen wani biki a yankin Nangarhar, Afghanistan
- Sojojin kungiyar Taliban sun bude wuta ne saboda an kunna wake-wake a wajen wannan bikin.
- Mai magana da yawun bakin kungiyar a kasar Afghanistan, Zabihullah Mujahid, ya fitar da jawabi.
Afghanistan - Akalla mutane biyu da suka halarci wani daurin aure a gabashin kasar Afghanistan aka kashe a ranar Juma’a, 29 ga watan Nuwamba, 2021.
CNN ta fitar da rahoto a makon nan, tace an kashe wadannan Bayin Allah ne saboda sun saurari waka.
Ana zargin wasu ‘yan kungiyar Taliban da wannan aika-aika, inda suka budawa masu halartar wannan biki wuta. Hakan ya yi sanadiyyar rasa Bayin Allah.
Mai magana da yawun bakin Taliban, Zabihullah Mujahid ya zanta da ‘yan jarida a ranar Lahadi, yace wadanda suka yi kisan suna jingina kansu da kungiyar.
Da yake jawabi a gaban ‘yan jarida, Mujahid yace ‘yan bindigan sun yi wannan ta’adi ne a wajen wata walima da aka shirya a Surkh Rod, a yankin Nangarhar.
Rahotanni sun zo cewa an kashe mutane biyu ne a harin, yayin da aka bar sama da goma da rauni.
Addini yace a kashe wanda ya ji waka?
Kakakin kungiyar Taliban na kasar ya yi tir da aikin ‘yan bindigan, yace bai halatta a kashe wani saboda ya saurari wake-wake, yace ana bincike kan lamarin.
Mujahid yace a musulunci, babu wanda yake da ikon ya hana mutane jin waka, sai dai ya yi masu wa’azi, ya tabbatar da cewa za a gano abin da ya jawo kisan.
A shari'ar addinin musulunci babu inda aka ce a zartar da hukuncin kisa ga wanda ya saurari waka.
Babu tabbacin cewa wadanda suka yi kisan ‘ya ‘yan Taliban ne, amma dai an cafke ‘yan bindiga biyu. Sai dai wani ‘dan bindigan ya tsere yayin da ake bincike.
A wani rahoto da NBC ta fitar, tace ‘yan bindigan sun yi wa masu bikin magana da kakkausar murya a kan sauraron wake-wake, kafin su buda masu wuta.
Hosea Ehinlanwo ya bar Duniya
A yau ake jin cewa jam’iyyar PDP ta na zaman makoki yayin tsohon 'dan majalisarta, Sanata Hosea Ehinlanwo,ya rasu yana da shekara 83 da haihuwa.
Tsohon jigon na PDP ya rasu kwanaki kadan da yin zaben shugabannin jam’iyya na kasa. Hosea Ehinlanwo ne ya fara bijiro da maganar Obasanjo ya zarce.
Asali: Legit.ng