Dadi kamar ya kashe su: Kotu tace Gwamnatin Tarayya ta biya jihar Delta Naira Biliyan 670
- Babban kotun tarayya mai zama a garin Abuja ta zartar da hukunci a kan wata shari’a da ke gabanta.
- Mai shari'a Donatus Okorowo ya bukaci Gwamnatin tarayya ta biya jihar Delta wasu kudi fam $1.6bn.
- Lauyoyi sun ce wannan kason jihar ne a wasu kudi da Najeriya ta samu a matsayinta mai arzikin mai.
FCT, Abuja - A ranar Litinin, 1 ga watan Nuwamba, 2021, babban kotun tarayya da ke zama a garin Abuja ya bukaci a biya jihar Delta Dala biliyan $1.638.
Alkalin babban kotun, Donatus Okorowo yace gwamnatin tarayya ta biya jihar Delta wannan kudi.
Jaridar Vanguard ta rahoto Mai shari’a, Donatus Okorowo yana cewa ya gamsu cewa kason jihar Delta da ake ba jihohi masu arzikin mai, ya taru ya kai $1.638b.
Rahoton yace an tara bashin hakkin jihar Delta daga kason 13% da ake cirewa daga dukiyar man fetur, ake ba duk wata jiha da ake hako danyen mai a cikinta.
Da yake zartar da hukunci a ranar Litinin a shari’ar mai lamba FHC/ABJ/CS/660/2012, Donatus Okorowo yace ba a kalubalanci wannan kara da aka kawo ba.
Ken Njemanze SAN ya je kotu
Delta ta shigar da kara ta hannun Cif Ken Njemanze SAN, yana neman a tursasawa AGF ya biya jihar 5% daga cikin wasu Dala biliyan 50 da Najeriya ta samu.
Ken Njemanze SAN ya roki kotu ta sa babban akawun gwamnati ya biya gwamnatin jihar Dala biliyan 1.638 daga cikin wannan kudi a matsayin na ta kason.
Haka zalika Mai shari’a, Donatus Okorowo ya hada da 10% a matsayin ruwan da bashin ya tara. Jaridar The Eagle ta tabbatar da wannan rahoto a makon nan.
Wani martani gwamnatin tarayya tayi?
Sai dai babban lauyan gwamnatin tarayya ya shigar da korafi a gaban kotun, yana rokon Alkali ya yi fatali da wannan kara da aka shigar domin ba ta da karfi.
Wani jami’i a ma’aikatar shari’a ta kasa, Thomas Etah, ya shigar da wannan kara a madadin AGF, yana cewa sam jihar Delta ba ta cikin wadanda za a biya kudin.
A karshe Alkali ya yarda gwamnatin tarayya ta biya gwamnatin Delta wannan bashi da yake wuyanta, ya na mai watsi da bukatar da Etah ya gabatar gabansa.
Shehu Sani ya caccaki Gwamnatin tarayya
Kwamred Shehu Sani ya caccaki Gwamnatin APC a kan kin ayyana ‘Yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda, duk da kiraye-kirayen da jihohi da sauran jama'a suke yi.
Tsohon Sanatan ya yi wa masu mulki gatse a shafinsa na Twitter a ranar Litinin, yana cewa sai a ayyana 'yan bindiga a matsayin ma'aikatan gwamnatin tarayya.
Asali: Legit.ng