Na halarci taron sauyin yanayi a Glasgow, kuma na gana da Yariman Ingila, Shugaban Faransa dss

Na halarci taron sauyin yanayi a Glasgow, kuma na gana da Yariman Ingila, Shugaban Faransa dss

  • Isarsa ke da wuya da safiyar Litnin, Shugaba Buhari ya halarci taron shugabannin duniya da na majalisar dinkin duniya
  • Hotuna sun bayyana yadda shugaban kasar Najeriyar ke tattaunawa da Shugabannin kasashe daban-daban
  • A ranar Talata kuwa, an shirya Shugaba Buhari zai gabatar da wani jawabi na musamman

Birtaniya - Shugaba Muhammadu Buhari ya halarci taron neman mafita kan lamarin sauyin yanayi a duniya na majalisar dinkin duniya dake gudana yanzu a birnin Glasgow, Scotlan, Birtaniya.

Buhari ya hadu sauran shugabannin duniya da suka zo wakiltan kasashensu domin neman mafita kan lamarin sauyin yanayi don amfanin duniya.

Legit ta tattaro Shugaban kasan da kansa ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook da yammacin Litinin, 1 ga Nuwamba, 2021.

Na halarci taron COPS24 a Glasgow
Na halarci taron sauyin yanayi a Glasgow, kuma na gana da Yariman Ingila, Shugaban Faransa dss Hoto: Aso Rock Villa
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya tafi Birtaniya, daga nan kuma zai tafi Faransa

Shugaba Buhari yace:

"Na halarci taron Shugabannin duniya na sauyin da yanayi da majalisar dinkin duniya ta shirya #COP26 a Glasgow, Scotland, yau."
"Hakazalika na yi jawabi a wani taro daban kan "Gaggauta dawo da filaye a Afrika," tare Shugaban kasar Faransa, Yariman Ingila da Shugaban kasan Mauritania."

Sai kuma wani taro?

Buhari ya kara da cewa ya zanna da babba jami'in majalisar dinkin duniya kan yaki da sare itatuwa da sauran su.

"Bayan haka kuma nayi ganawar diflomasiyya da Sakataren majalisar dinkin duniya kan yaki da sare maishe da gari Sahara, Mr. Ibrahim Thiaw.," a cewarsa.

Shugaba Buhari ya dira birnin Glasgow, Kasar Birtaniyya da asubancin Litinin

Hadimin Shugaban kasan na kafafen talabijin da rediyo, Buhari Sallau, ya bayyana hakan ne a bidiyon da ya saki ranar Litinin, 1 ga Nuwamba, 2021.

Buhari zai gabatar da jawabi a taron ga shugabannin kasashen duniya ranar Talata, 2 ga Nuwamba, 2021.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Shugaba Buhari zai tafi Birtaniya yau Lahadi, daga nan kuma ya tafi Faransa

Daga nan kuma zai garzaya Faransa

Garba Shehu ya bayyana cewa bayan taron sauyin yanayi a Birtaniya, Shugaba Buhari zai tafi kasar Faransa domin halartan taron zaman lafiya a Paris.

Yace:
"Shugaba Buhari daga baya zai tafi Paris, Faransa domin ziyara ga Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, domin nuna godiya bisa ziyarar da Shugaban kasan Faransan ya kawo Najeriya a baya."

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng