Da Dumi-Dumi: An fara zaro gawarwakin mutane daga gini mai hawa 21 da ya rushe a Najeriya
- Jami'an hukumar agaji NEMA sun samu nasarar gano gawar mutum uku daga cikin dogon ginin da ya rushe a jihar Legas
- Hakanan an kuma ceto wasu mutum uku da suke da sauran numfashi a gaba, suna asibiti ana kulawa da lafiyarsu
- Wani dogon gini da ba'a kammala ba ya ruguje kan mutane a ƙan hanyar Gerald dake Anguwar highbrow, jihar Legas
Lagos - Jaridar Dailytrust ta rahoto cewa aƙalla gawar mutum uku aka gano zuwa yanzun daga ɓaraguzan gini mai hawa 21 da ya rushe a jihar Legas ranar Litinin.
Babban ginin, wanda ake cikin ginawa, ya ruguje ne a kan hanyar Gerald dake yankin Anguwar highbrow a jihar Legas.
Shugaban hukumar bada agajin gaggawa, NEMA, Ibrahim Farinloye, yace an matsar da gawarwakin zuwa ɗakin ajiye gawa mallakin gwamnatin jihar Leagas.
Mista Farinloye yace:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Jami'ai sun gano gawarwakin ne daga ƙarƙashin wasu ɓaraguzan ginin da ya rushe."
Shin an gano wasu da rai?
Hukumomi sun tabbatar da cewa an samu nasarar ceto wasu mutum uku da ransu, kuma yanzu haka suna asibiti ana kula da lafiyarsu.
PM News ta rahoto ragujewar ginin a ranar Litinin, amma tace har yanzu da ake tattara labarin, babu cikakken labari game da yanayin da ake ciki.
Matasa sun mamaye majalisar Filato
A wani labarin na daban kuma Zanga-Zangar Matasa a majalisar dokokin Filato ta dauki sabon salo, An fara harbe-harbe
A halin yanzun wasu matasa da ake tsammanin magoya bayan sabon kakakin majalisa ne, Yakubu Sanda, sun kutsa kai cikin zauren ta kofar baya.
Hakan ya harzuƙa magoya bayan tsohon kakaki, amma jami'an tsaro suka fara harbi a iska domin kwantar da tarzomar.
Asali: Legit.ng