Dinbin mutane sun makale carko-carko yayin da gini mai hawa 20 ya ruguje a Najeriya
- Wani gini mai tsawon hawa 20 ya ruguje a titin Gerald Road da ke yankin highbrow area a Ikoyi, Legas.
- Hukumar bada agajin gaggawa na jihar Legas ta tabbatar da cewa wannan gini ya ruguje a yau da rana.
- Shugaban hukumar LASEMA, Dr. Femi Oke-Osanyintolu bai da cikakken bayanin abin da ya faru.
Lagos - Labari maras dadi yana zuwa mana cewa wani dogon gini ya ruguje a garin Ikoyi, jihar Legas, a kudu maso yammacin Najeriya.
Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Litinin, 1 ga watan Nuwamba, 2021, cewa wannan dogon gini da ke unguwar Ikoyi ya kife dazu da rana.
Rahotanni sun tabbatar mana cewa wannan zungureren gini da yake yankin Alexandria Avenue a unguwar ta Ikoyi ya na da tsawon hawa 20.
A lokacin da jaridar Daily Trust ta fitar da rahoton, ba ta samu labarin adadin mutanen da suka samu rauni ko jikkata daga wannan hadari ba.
Jaridar PM News ta kawo irin wannan rahoto, amma tace har yanzu da ake tattara labarin, babu cikakken labari game da yanayin da ake ciki.
Shugaban hukumar LASEMA ta yi magana
Da aka tuntubi shugaban hukumar bada agajin gaggawa na jihar Legas, LASEMA, Dr. Femi Oke-Osanyintolu, ya tabbatar da lallai ne ginin ya rushe.
Dr. Femi Oke-Osanyintolu yace ba zai iya cewa mutane suna cikin ginin a lokacin da abin ya faru ba, ko kuma wannan ginin kango ne a halin yanzu.
Shugaban hukuar LASEMA, ya iya tabbattar da cewa an tura jami’ai domin su bada agajin gaggawa.
Wata majiyar ta tabbatar da cewa jami'an hukumar NEMA na kasa da na LASEMA da motocin kwana-kwana na kashe gobara sun isa wannan wuri.
Bola Tinubu zai yi takara a 2023?
Bayan kafa kungiyar Tinubu Support Group, sai aka ji an kaddamar da Patriots of Bola Ahmed Tinubu da nufin yi wa tsohon gwamnan Legas kamfe.
POBAT za ta bi lunguna-lunguna domin Bola Tinubu ya karbi mulkin Najeriya. Patriots of Bola Ahmed Tinubu tace lokaci ya yi da mulki zai koma Kudu.
Asali: Legit.ng