2023: Masoyan Tinubu sun dage, sabuwar kungiya ta fara jawowa jigon APC mutane a Jihohi 36

2023: Masoyan Tinubu sun dage, sabuwar kungiya ta fara jawowa jigon APC mutane a Jihohi 36

  • POBAT ta kaddamar da yakin neman zaben Bola Tinubu a Graceland Gardens and Park event hall a Abuja
  • Kungiyar Patriots of Bola Ahmed Tinubu tana ganin ya kamata mulkin Najeriya ya koma hannun ‘Yan Kudu
  • Dr Babatunde Bello yace POBAT za ta dage domin ganin Jigon na APC ya gaji Muhammadu Buhari a 2023

Abuja - Kwanaki kadan da kaddamar da kungiyar Tinubu Support Group, sai aka ji wasu magoya baya sun fito da tafiyar Patriots of Bola Ahmed Tinubu.

Jaridar Daily Trust tace magoya bayan Asiwaju Bola Tinubu sun fito da wata sabuwar kungiya mai suna Patriots of Bola Ahmed Tinubu watau POBAT.

An kaddamar da wannan kungiya ta POBAT ne a babban birnin tarayya Abuja. Taron ya samu halartar ‘yan kungiyar daga duka jihohin fadin kasar nan.

Kara karanta wannan

Labari Cikin Hotuna: Jagoran Jam'iyyar APC Bola Tinubu ya dira Fadar Shugaba Buhari Aso Villa

Shugaban kungiyar POBAT na kasa, Dr Babatunde Bello ya yi jawabi a wajen bikin, yace Najeriya tana bukatar shugaba irin Bola Tinubu ya hau mulki a 2023.

Vanguard ta rahoto Babatunde Bello yana cewa POBAT za ta dage domin ganin Tinubu ya karbi mulki.

Manyan APC
Bola Ahmed Tinubu a taron APC Hoto: www.theyorubablog.com
Asali: UGC

Babatunde Bello yace yanzu aka fara

“Ba na tantama cewa POBAT tana cikin tulin kungiyoyin da suke goyon bayan Asiwaju Bola Ahmed (Tinubu) ya karbi mulki.” - Dr. Babatunde Bello.
"Bayan wannan kaddamarwar, za mu zama ‘yan gaba-gaba wajen goyon bayan takararsa. Za mu karada kasar nan domin nema masa goyon baya."

Tinubu ne zabin mu - Dr Abiola Oshodi

Shi ma jagoran POBAT na kasa, Dr Abiola Oshodi yace sun gamsu lokaci ya yi da shugabancin Najeriya zai koma Kudu, kuma Tinubu ya dace ya rike kasa.

Kara karanta wannan

2023: Fitattun 'yan siyasan Najeriya 11 da suka ce sai Tinubu

“Mun yi amanna yanzu ne lokacin da Kudu za su fito da shugaban kasa. Kuma aikinmu ne mu dage wajen ganin Tinubu ya karbi mulki.” – Oshodi

Shugaban kungiyar SWAGA, Adedayo Adeyeye, ya yi jawabi a wajen wannan bikin da aka shirya a Graceland Gardens & Park event hall a unguwar Wuse.

Kwankwaso zai bar PDP kafin 2023?

Kuna sane cewa an dade ana jita-jitar tsohon Gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso zai iya ficewa daga PDP, ya koma jam'iyyar APC da ya baro kafin zaben 2019.

Babban ‘dan siyasar ya yi magana game da wannan rade-rade da rigingimun da suka addabi tsaginsu, inda ya tabbatar da cewa har gobe yana nan a PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel