Labari Cikin Hotuna: Bola Tinubu ya dira Aso Villa, Yace shugaba Buhari na musamman ne
- Jigon jam'iyyar APC mai mulki, Asiwaji Bola Ahmed Tinubu, ya ziyarci shugaban ƙasa Buhari a fadarsa dake Abuja
- Tinubu ya bayyana cewa ya zo yi wa shuagaban ƙasa Buhari godiya ne bisa ziyarar da yakai masa a Landan bayan an masa tiyata
- Rahotanni sun tabbatar da cewa manyan mutanen biyu sun gana da juna a sirrance ya yin wannan ziyara
Abuja - Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya karbi bakuncin jagoran jam'iyyar APC, Bola Tinubu, a fadarsa dake Abuja, ranar Lahadi da safe.
Mai taimakawa shugaban ƙasa Buhari ta ɓangaren yaɗa labarai, Bashir Ahmad, shine ya sanar da haka a shafinsa na dandalin Facebook.
Bashir Ahmad ya rubuta kamar haka:
"Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin jagoran babbar jam'iyyar mu APC, Asiwaju Bola Tinubu, a gidan gwamnati dake Abuja, da safiyar yau."
Sai dai rahotanni daga fadar ta shugaban ƙasa sun bayyana cewa manyan mutanen biyu sun sa labule, wato sun gana da sirrance.
Meya kai Tinubu wurin Buhari?
Bayan taron na su ne, Tinubu ya bayyana cewa ya kawo wa Buhari wannan ziyara ne domin ya gode masa bisa ziyarar da yakai masa a Landan lokacin da yake jinya.
Tinubu yace:
"Na zo na miƙa godiyata ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari bisa ziyarar da ya kai min lokacin da aka mun tiyata a guiwa. Ya nuna mun kulawarsa da kuma jajanta mun, shi na daban ne."
Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton lokacin da shugaba Buhari ya ziyarci Bola Tinubu a Landan tun a watan Augusta.
Hotunan zuwa Tinubu Aso Villa
A wani labarin kuma yayin da ake Rade-Radin sauya shekar Jonathan zuwa APC, An gano babban dalilin da ya hana shi halartan gangamin PDP
Rahoto ya bayyana cewa Jonathan ya faɗa wa gwamnonin PDP biyu da suka ziyarce shi cewa ba zai halarta ba saboda zai bar Najeriya.
Gwaamnonin sun roki babban jigon na PDP da ya halarci wurin kuma ya bada jawabinsa kafin ya kama hanyar fita kasar, amma ya yi watsi da bukatarsu.
Asali: Legit.ng