Shugaban EFCC ya magantu kan samamen da jami'an tsaro suka kai gidan Mary Odili

Shugaban EFCC ya magantu kan samamen da jami'an tsaro suka kai gidan Mary Odili

  • Abdulrasheed Bawa, shugaban EFCC ya musanta hannun hukumar wurin samamen da aka kai gidan Mary Odili
  • Bawa ya ce wasu masu gutsiri tsoma ne ke son ganin sun lalata alakar hukumar da bangaren shari'a
  • Ya tabbatar da cewa hatta hukumomin da ke da alaka da su ya kira kuma sun tabbatar da babu hannunsu

FCT, Abuja - Shugaban hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta yi tsokaci kan samamen da jami'an tsaro suka kai gidan mai shari'a Mary Odili.

Jami'an tsaro sun shiga gidan alkalin kotun kolin da ke Maitama a ranar Juma'a, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Shugaban EFCC ya magantu kan samamen da jami'an tsaro suka kai gidan Mary Odili
Shugaban EFCC ya magantu kan samamen da jami'an tsaro suka kai gidan Mary Odili. Hoto daga Femi Adesina
Asali: Facebook

Akwai rahotanni da ke yawo na cewa hukumar EFCC na da hannu kan samamen amma daga bisani hukumar ta tsame kanta daga ciki.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Jami'an tsaro sun dira gidan alkalin kotun koli a Abuja

A yayin zantawa da gidan talabijin na Channels, Bawa ya ce kokarin alakanta hukumar EFCC da wannan samamen duk aikin makaryata ne.

Ya ce wadanda ke fadin hakan su na kokarin lalata alakar da ke tsakanin fannin shari'a ne da na hukumar.

Bawa ya ce, "Ina tunanin masu gutsiri tsoma ne da ke son alakanta komai da EFCC. Ba mu je ba kuma babu wani jami'in mu da ya je. Ba daga EFCC suke ba kuma ba lamarin EFCC ba ne.
"Sannan na kira dukkan hukumomin da ba na tsaro ba da ke kasar nan kuma sun musanta hannunsu ko na jami'ansu da zuwa duba gidanta ko kama ta.
"A takaice dai, na samu labarin cewa wani bbabban lauya ya kira daraktan shari'armu. Mu na taro ne da yammacin kuma ya ce a bai wa daraktan ayyuka wayar sai dai kuma duk taron mu ke yi da yammacin.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Kotu ta hana Secondus dakatar da gangamin taron PDP na ƙasa

"Kuma da na dawo, saboda na fita a lokacin, sun tambaye ni me ke faruwa. Sai dai dariya kawai muka yi saboda mun gane cewa akwai mutane masu yawa da ke son hada mu rigima da fannin shari'a.
“Kuma ka san a aikin da muke yi, fannin shari'a ne manyan kawayenmu, kuma tabbas ana kokarin samar mana da matsala ne inda ba mu da ita."

Peter Odili, shi ne mijin alkalin kuma tsohon gwamnan jihar Ribas ne.

Jami'an tsaro sun dira gidan alkalin kotun koli a Abuja

A wani labari na daban, jami'an tsaro a ranar Juma'a sun dira gidan Mary Odili, alkali a kotun koli da ke Abuja. Alkalin kotun kolin mata ce ga Peter Odili, tsohon gwamnan jihar Ribas wanda a halin yanzu ya ke cikin wadanda hukumar yaki da rashawa ta kasa, EFCC suka sanya wa ido.

Kamar yadda TheCable ta wallafa, Har yanzu dai babu cikakken bayani kan abinda ke faruwa a gidan.

Kara karanta wannan

ICPC: Yadda muka kwato gidaje 301 daga jami'an gwamnati 2 a Abuja

Kamar yadda wata majiya ta ce, jami'an tsaron da suka tsinkayi gidan sun hada da jami'an 'yan sanda da na sojojin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng