Sheikh Dahiru Bauchi ya yaye sabbin mahaddatan Al-Qur'ani kimanin 2,500 a Bauchi
- Kamar yadda aka saba lokaci bayan lokaci, babban Malamin addini kuma jagoran Tijjaniya Sheikh Dahiru Bauchi ya yaye dalibai
- Sheikh Dahiru Bauchi na da dalibai da manyan makarantu a jihohin Najeriya daban-daban inda ake haddar Al-Qur'ani
- Malamin ya ja hankalin daliban kan muhimmancin bibiyar abinda suka haddace akai-akai
Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya sake yaye dalibai 2,438 da suka kammala haddar Al-Qur'ani mai girma da kuma dalibai 226 suka sauke karatun amma basu haddace ba.
Aminiya ta ruwaito cewa wadannan dalibai sun yi karatu ne a makarantun babban Malamin dake ciki da wajen Najeriya.
Daliban jihohin Najeriya daban-daban ne aka yaye a wannan bukin Walima.
Jihohi da adadin dalibansu
Jihar Bauchi: Mahaddata 534, masu sauka 226
Jihar Katsina: Mahaddata 499
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jihar Kano: Mahaddata 385
Jihar Kaduna: Mahaddata 257
Jihar Jigawa: Mahaddata 186
Jihar Sakkwato: Mahaddata 168
Jihar Zamfara: Mahaddata 152
Babban Malamin ya samu wakilcin babban dansa, Ibrahim Sheikh Dahiru, a taron.
Ya ja hankalin daliban su kara zage damtse domin inganta tilawarsu, inda ya ce Alkur’ani abu ne da in mutum ya sauke ko ya haddace ana so kullum ya rika bibiyarsa yana yawan karantawa.
Asali: Legit.ng