Shugaba Buhari ya amince a gina asibiti mai gado 14 a kudi N21.9billion a Aso Villa

Shugaba Buhari ya amince a gina asibiti mai gado 14 a kudi N21.9billion a Aso Villa

  • Bayan asibitin dake fadar shugaban kasa, za'a sake ware kimanin bilyan 22 don gina wani sabon asibiti
  • Wannan sabon asibiti mutum 14 kadai zasu iya kwanciya jinya ciki kuma ba na gama-garin jama'a bane
  • Shugabannin kasashen Afrika dake bukatan zuwa zasu iya jinya a asbitin

Abuja - Shugaba Buhari ya amince da a gina sabon asibiti mai gado 14 kacal a fadar shugaban kasa Aso Villa a kudi N21 billion.

Sakataren din-din-din na fadar shugaban kasa, Umar Tijjani, ya bayyana hakan ga mambobin kwamitin daidaito na majalisar dattawa yayin bayani kan kasafin kudin N40 billion na fadar shugaban kasa.

ChannelsTV ta ruwaito cewa ya yi bayanin cewa tun shekarar 2012 aka shirya gina asibitin amma yanzu za'a cigaba da ginin.

Yace:

"Tun 2012 gwamnatin baya ta yi shawaran ginin. An yi lissafin cewa za'a kashe N21.9 billion kuma asibitin zai kunshi gado 14."

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya zata karbi bashin N290bn don samarwa yan Najeriya ruwan sha

"Tuni an kammala ayyukan farko."

z'aa gina asibiti mai gado 14 a kudi N21.9billion a Aso Villa
Shugaba Buhari ya amince a gina asibiti mai gado 14 a kudi N21.9billion a Aso Villa Hoto: Aso Villa
Asali: UGC

Wani kamfani za'a baiwa kwangilan kuma yaushe za'a kammala?

Umar Tijjani ya bayyana cewa kamfanin Julius Berger Nigeria, JBN, aka baiwa kwangilan ginin asibitin kuma za'a fara ginin ranar 1 ga Nuwamba, 2021, riwayar DailyNigerian.

Ya bayyanawa kwamitin cewa an zabi baiwa JBN kwangilan ne saboda su suka gina fadar shugaban kasan kuma suke kula da ita tun shekarar 1990.

Ya kara da cewa za'a kammala ginin cikin shekara guda kuma a bude asibitin ranar 31 ga Disamba, 2022.

Me da me asibitin zai kunsa?

Sakataren ya ce asibitin mai gado 14 ne kacal kuma zai kunshi dakunan Tiyata biyu, dakunan kwantar da shugaban kasa 2, dakunan manyan mutane 2, dakunan killace mara lafiya 2, da kuma dakin killace mutum shida guda 1.

Kara karanta wannan

Majalisar dattawa tayi Alla-wadai da shirin karban bashin N290bn don samar da ruwan sha

Hakazalika za'a gina dakin bincike daya, dausayin shakatawa na mara lafiya, dakin ajiye magunguna, da dakin daukan hoto.

Yace bayan shugaban kasa, sauran shugabannin kasashen Afrika zasu iya zuwa jinya asibitin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng