Fani-Kayode: Gumi ya fi Shekau da Al-Barnawi ta'addanci, maciji ne mai dafi kuma ungulu da kan zabo
- Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode ya ce Sheikh Gumi ya fi Shekau da Al-Barnawi ta'addanci
- Cike da fusata da fitaccen malamin Islaman, Fani-Kayode ya ce babu shakka Gumi maciji ne mai matukar dafi kuma ungulu da kan zabo
- Dan siyasan ya caccaki Gumi ne kan kiran da yayi ga gwamnatin tarayya da kar ta yi kuskuren ayyana 'yan bindiga da 'yan ta'adda
Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode ya caccaki fitaccen malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi kan matsayarsa a kiran da ake ta yi wa gwamnati na ayyana 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda.
Fitaccen malamin ya gargadi gwamnatin tarayya da kar ta kuskura ta tafka wannan kuskuren saboda abinda zai iya zuwa ya dawo.
Fani-Kayode ya zargi cewa, mahaifin fitaccen malamin, Sheikh Abubakar Mahmud Gumi ya taba cewa kada a kuskura Kirista ya mulki Najeriya.
Tsohon ministan da bai dade da sauya sheka ba zuwa jam'iyya mai mulki, ya ce malamin ya fi marigayin shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau da Al-Barnawi ta'addanci.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Dan siyasan ya kara da kwatanta Gumi da "maciji mai matukar dafi kuma ungulu da kan zabo."
Kamar yadda tsohon ministan ya wallafa rubutu tare da hoton malamin a shafinsa na Instagram:
"Sheikh Ahmad Gumi Rasputin arewa, wanda mahaifinsa ya taba cewa kada a kuskura Kirista ya mulki Najeriya kuma shi da kan shi ya ce kada gwamnatin tarayya ta ayyana 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda.
"Ya fi Abubakar Shekau da Al Barnawi ta'addanci. Maciji ne mai matukar dafi kuma ungulu da kan zabo ne."
Ku tattauna da Igboho, IPOB kamar yadda na ke yi da 'yan bindiga, Gumi ga malaman kudu
A wani labari na daban, Sheikh Ahmad Gumi ya bukaci malaman kudancin kasar nan da su tashi tsaye wurin tattaunawa da masu tada kayar baya tare da assasa rashin tsaro a yankunansu kamar yadda ya ke wa 'yan bindiga.
Fitaccen malamin ya sanar da hakan ne yayin da ya ke fitar da takarda kan martaninsa ga masu bukatar gwamnatin tarayya ta ayyana 'yan bindiga da 'yan ta'adda, Daily Trust ta ruwaito.
A makon da ya gabata, Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya sake bukatar gwamnatin tarayya da ta bayyana 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda.
Asali: Legit.ng