A karon farko, an samu kungiyar da ta yi gagarumin biki domin bunkasa harshen Hausa
- Open Arts ta shirya bikin bajakolin fasahohi da littatafan Hausawa da aka yi a Kaduna
- Marubutan Arewacin Najeriya da ‘yan wasan kwaikwayo da taurari sun halarci taron
- Cikin wadanda suka ba taron armashi har da uwargidar jihar Kaduna, Hadiza El-Rufai
Kaduna - Tsakanin ranar 21 ga watan Satumba zuwa 23 ga watan Satumba, 2021, aka shirya wani bikin bajakolin fasahohi da littatafan Hausawa a garin Kaduna.
Legit.ng Hausa ta samu labari an yi wa bikin Hausa International Book and Arts Festival (HIBAF) wanda shi ne karon farko a Najeriya na shekarar nan taken ‘sarari’
Open Arts a karkashin Sada Malumfashi da ta shirya wannan biki, ta kawo ‘yan wasan fim, marubuta, mawaka da sauran wadanda suka taimakawa adabi.
Bikin ya samu halartar fitattun masana da malamai daga fadin Najeriya har da kasashen ketare. An ba Umaru Danjuma kyauta ta musaman a wajen wannan biki.
Farfesoshi da marubuta sun ba taron armashi
An fara taron da wata tattaunawa da aka yi a kan wanene Bahaushe. Farfesa Ibrahim Malumfashi ne ya jagoranci wannan zama tare da Farfesa Abdalla Uba Adamu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Malam Khalid Imam ne ya jagoranci zaman da aka yi da wasu fitattun matasan marubutan zamanin yau; Maryam Sokoto, Fatima El-Ladan da Saleem Yunusa.
An ga tsohuwar marubuciya da fasihin makahon mawaki
Malam Yahaya Makaho ya samu halartar HIBAF, inda ya rangadawa mahalarta wasu wakokinsa. Matasa sun kuma samu damar haduwa da Hafsah Abdulwaheed.
A ranar Alhamis ne Malam BM Dzukogi, Sumayya Ja’eh da Halima Aliyu suka tattauna da Dima Chami a kan gwargwarmayar rubuce-rubuce a Arewacin Najeriya.
Taron ya kuma samu halartar marubuta da mawaka irinsu Bilkisu Yusuf Ali, Rahma Majid, Halima Matazu, Halima Ahmed, Sani Liya-liya tare da Dr. Halima Daura.
Ado Ahmad Gidan Dabino, Balaraba Ramat Yakubu da taurari kamar Abubakar Ladan watau Alan Waka duk sun halarci wannan taro,inda suka nuna irin kwarewarsu.
Salisu Usman Yusuf ya jagoranci zaman da aka ayi da Samuel Aruwa. Har ila yau, Farfesa Audi Giwa ya tattauna da marubuta; Hadiza Isma El-Rufai da Richard Ali.
Asali: Legit.ng