Jerin tituna 21 da za su ci makudan kudade, kuma gwamnatin Buhari ta amince a yi

Jerin tituna 21 da za su ci makudan kudade, kuma gwamnatin Buhari ta amince a yi

A yayin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da koke-koke kan lalacewar tituna, hukumar kula da harkokin man fetur ta kasa (NNPC) ta yi yunkuri wajen gyara wasu tituna 21 na tarayyar kasar a dukkan shiyyoyin siyasar kasar nan guda shida.

Matakin na NNPC wanda aka kiyasta zai ci Naira biliyan 621.2 ya samu amincewar Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) a ranar Laraba 27 ga watan Oktoba.

The Cable ta ruwaito cewa Babatunde Fashola, ministan ayyuka da gidaje ne ya bayyana haka bayan taron FEC da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta.

Ministan ya bayyana cewa an amince da bukatar da NNPC ta gabatar ne bisa tsarin zartarwa mai lamba 007 na shekarar 2019 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya wa hannu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta amince da biyan kudin kammala titin Gombe zuwa Biu

FEC ta amince da bukatar kamfanin NNPC na gyara titunan gwamnatin tarayya 21 a shiyyar siyasa 6, zai ci N621bn
Taron majalisar zartarwa (FEC) | Hoto: Aso Rock Villa
Asali: Facebook

A cewarsa, Dokar Zartarwa ta 7 ta ba wa kamfanoni masu zaman kansu damar biyan harajin da za su biya a gaba don bunkasa ababen more rayuwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kara da cewa, hanyoyin da aka zabo guda 21 na da nisan kilomita 1804.6, kuma wannan shiri ne na dabara a karkashin shirin gwamnatin tarayya na samar da ababen more rayuwa da samar da karin haraji, inji NNPC.

Legit.ng ta tattaro cewa tara daga cikin ayyukan da aka zaba za a yi su ne a arewa ta tsakiya, uku a arewa maso gabas, biyu a arewa maso yamma, biyu a kudu maso gabas, uku a kudu maso kudu, biyu kuma a kudu maso yamma.

A kasa mun kawo muku cikakken jerin hanyoyin:

Arewa ta tsakiya

  1. Mayar da titin Ilorin-Jebba-Mokwa/Marabar Bokani sashi na I zuwa titi mai hannu biyu a jihar Kwara, nisan kilomita 110.8
  2. Mayar da titin Ilorin-Jebba-Mokwa/Marabar Bokani sashi na II zuwa titi mai hannu biyu a jihar Kwara, nisan kilomita 46
  3. Mayar da titin Suleja-Minna a jihar Neja zuwa titu mai hannu biyu, nisan kilomita 40, sashe na I
  4. Mayar da titin Suleja-Minna a jihar Neja zuwa titu mai hannu biyu, nisan kilomita 61, sashe na II
  5. Sake gina titin Bida-Lambata a Jihar Neja, nisan kilomita 125
  6. Titin Agaie-Katcha-Baro na jihar Neja, nisan kilomita 52.3
  7. Gyaran gaggawa na sashin Mokwa-Makera-Tagina-Kaduna-Kaduna a jihar Neja, nisan kilomita 164
  8. Titin Minna-Zungeru minna-Zungeru-Tagina a jihar Neja, nisan kilomita 90
  9. Titin Bida-Minna shi ma a jihar Neja, nisan kilomita 791.1

Kara karanta wannan

PDP na bukatar mutane masu mutunci domin lashe zaben shugaban kasa a 2023 - Fintiri

Arewa maso gabas

  1. Gyaran sashen Cham-Numan na titin Gombe zuwa Yola a jihar Adamawa, nisan kilomita 46.35
  2. Gina hanyar Bali-Serti a jihar Taraba, nisan kilomita 110
  3. Gyaran titin Gombe-Biu a jihar Gombe/Borno, nisan kilomita 117

Arewa maso yamma

  1. Gyaran guraren da suka yi fice na titin Gada-Zaima-Zuru-Gamji, sashi II a jihar Kebbi, nisan kilomita 62
  2. Gyaran titin Zariya-Funtua-Gusau-Sokoto-Birnin Kebbi, nisan kilomita 221.5

Kudu maso kudu

  1. Gyaran titin Odukpani-Itu-Ikot Ekpene a jihar Kuros Riba Sashi na I: Gadar Odukpani-Itu a jihar Kuros Riba/Akwa Ibom, nisan kilomita 21.9
  2. Mayar da fitaccen yanki Odukpani-Itu-Ikot Ekpene zuwa mai hannu biyu: sashe na 2, nisan kilomita 32
  3. Mayar da titin sashen cibiyar wutar lantarki ta Oku-Iboku na titin Itu-Ikot-Ikpene zuwa mai hannu biyu a jihar Kuros Riba/Akwa Ibom, nisan kilomita 28

Kudu maso gabas

  1. Mayar da titin Aba-Ikot Ekpene zuwa mai hannu biyu a jihar Abia/Akwa Ibom, nisan kilomita 73
  2. Gyaran titin Umuahia (Ikwuano)-Ikot Ekpene: Umuahia-Umudike a jihar Abia, nisam kilomita 49

Kara karanta wannan

Sai mun hada kai ne za mu iya cin galaba a kan miyagu – APC kan harin jirgin kasa

Kudu maso yamma

1. Gyara da fadada titin Legas-Badagry (Mahadar Agbara-Nigeria/Iyakar Benin) a jihar Legas, nisan kilomita 62

2. Mayar da titin Ibadan-Ilorin zuwa mai hannu biyu (Route A2) Sashe na II a Jihar Oyo (Oyo-Ogbomosho), nisan kilomita 52

Gwamnatin Buhari ta amince da biyan kudin kammala titin Gombe zuwa Biu

A wani labarin, A ranar Talata ne gwamnatin tarayya ta ce za a samar da isassun kudade domin kammala dukkan manyan titunan gwamnatin tarayya a fadin kasar nan kan lokaci, ciki har da titin Gombe zuwa Biu.

Babban sakataren ma’aikatar ayyuka da gidaje Hassan Musa ne ya bada wannan tabbacin a Abuja yayin da yake jawabi ga shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar, Muktar Betara.

Ya ce ma’aikatar ta samu sabbin kudade na aikin hanyar Gombe zuwa Biu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.