Tun da maza sun gaza, Lokaci ya yi da zamu mika wa mata ragamar mulkin Najeriya, Gwamnan APC
- Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo, ya yi hasashen cewa mata zasu iya ceto Najeriya daga halin da take ciki a yanzun
- Gwamnan yace babu al'ummar da zata cigaba matukar ta yi watsi da mata domin mata jagorori ne nagari
- Yace tarihin Najeriya cike yake da jarumtar mata, kuma matukar ana son a cigaba sai an jawo su cikin harkar mulki
Ondo - Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, yace mata suna da kwarewar da zasu ceto Najeriya daga halin da ta tsinci kanta idan aka basu dama.
The Nation ta ruwaito cewa Gwamnan na ganin tun da maza sun gaza gyara Najeriya, wannan lokacin ne da ya dace mata su shugabanci kasar nan.
Gwamna Akeredolu ya yi wannan furucin ne yayin da yake jawabin buɗe babban taron mata (NWC), karo na 21, wanda ƙungiyar matan Legas (COWLSO) ta shirya.
Rahoto ya nuna cewa an yi wa babban taron matan na tsawon kwanaki uku taken "Mata mu farka," kamar yadda Leadership ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shin mata zasu iya shugabancin Najeriya?
A jawabin gwamnan yace:
"Bai kamata a watsar da mata ba matukar ana son cigaban Najeriya. Abinda ya dace shine ko dai a ɗakko su a basu muƙamai ko kuma a basu ragamar mulkin baki ɗaya."
"Maza sun kasa tafiyar da ƙasar nan yadda ya kamata, mazan sun gaza, ina ganin abubuwa zasu fi gyaruwa idan aka jawo mata."
"Ya kamata mata su wuce matakin rawa da waƙa a wurin taron yaƙin neman zaɓe na siyasa, ya dace su yi wani abu na daban."
Shin mata sun taɓa taka rawar gani a Najeriya?
A cewar gwamna Akeredolu, ya kamata a maida hankali wurin horad da ƴaya mata su san rawar da zasu iya takawa nan gaba domin gobensu.
"Tarihin Najeriya cike yake da ƙwazon mata saboda haka ya zama wajibi mu rinka yaba musu."
Babu wata al'umma da zata maida mata koma baya kuma ta yi tsammanin samun cigaba. Idan ana son Najeriya ta cigaba to ya zama wajibi mata su karbi ragamar ƙasar nan.
"Ni a shirye nake na zauna karkashin mulkin mata, ya kamata kowa ya shirya, domin mata sun iya jagoranci."
A wani labarin kuma Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi yace shi ya fi dacewa ya karbi mulkin Najeriya a hannun shugaba Buhari
Gwamnan yace nasarorin da ya samu a jihar Kogi, sune suka jawo hankalin yan Najeriya, har suke bukatar ya shugabanci ƙasa.
A cewarsa duk da lokacin bai kammala wa'adin mulkinsa na biyu ba, amma muradin ƙasa ya wuce na Kogi.
Asali: Legit.ng