Gwamnan Gombe ya bukaci a kwashe tubabbun 'yan Boko Haram a kaisu jami'ar soji
- Gwamnatin jihar Gombe ta bayyana bukatar dauke tubabbun 'yan Boko Haram daga jihar
- Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ne ya bayyana haka a ranar Talata a gidan gwamnati
- Ya koka kan yadda aka mayar da sansanin 'yan bautar kasa ta jihar wurin ajiye tubabbun 'yan ta'adda
Gombe - ShaharaReporters ta ruwaito cewa, Gwamna Muhammadu Yahaya na jihar Gombe ya ce 'yan Boko Haram da ke sansanin gyaran hali na 'yan Boko Haram da ke Kwami ta jihar Gombe ya kamata a mayar dasu jami'ar soji da ke Biu a jihar Borno.
Yahaya ya bayyana hakan ne a lokacin da yake karbar babban kwamandan runduna ta 3 da aka fi sani da Operation Safe Haven, Manjo Janar Ibrahim Ali, a gidan gwamnati ranar Talata.
Ya ce duk da samar da matsuguni ga shirin na Gwamnatin Tarayya, sansanin ya karbi bakuncin wadanda ba ‘yan asalin jihar ba, ya kara da cewa bai kamata a sanya jihar ta sha wahala wajen daukar irin wannan lamari ba.
Sansanin wanda ya gyara daruruwan tubabbun ’yan Boko Haram daga sassan Arewa-maso-Gabas, wuri ne da gwamnatin jihar ta gina wa masu yi wa kasa hidima a matsayin sansani.
Yahaya ya ce:
“Gombe ta kwashe shekaru shida tana karbar bakuncin gyaran 'yan ta'adda."
Yahaya ya bayyana cewa, a farko an tsara shirin karbar bakuncin ne na watanni shida, amma ya lura cewa, batun ya so sauyawa zuwa na dindindin.
Ganin haka, gwamnan ya ce gwamnatin Gombe ba za ta iya ci gaba da lura da wannan aikin ba.
A cewarsa, kasancewarsu a jihar Gombe ya jefa jihar cikin wahalhalu da suka shafi noma da sauran lamurran yau da kullum
Zai yi wahala a karɓi tubabbun 'yan Boko Haram a cikin garuruwan mu – Shehun Borno
Shugabannin gargajiya da na addini a Borno sun ce zai yi wahala a sake karbar 'yan Boko Haram da suka tuba cikin garuruwa su.
Shugabannin sun bayyana fargaba kan yadda sojojin Najeriya za su raba tubabbun 'yan Boko Haram da tsattsauran ra'ayi a karkashin shirin su na Safe Corridor, jaridar The Cable ta ruwaito.
Abubakar El-Kanemi, Shehun Borno, ya ce wannan abu ne mai kyau, amma mutane za su ci gaba da kasancewa cikin fargaba na bala'in tashin hankalin da aka shafe shekaru 12 ana yi, musamman mazauna garuruwan da za a mayar da masu tayar da kayar bayan.
A tura 'yan Boko Haram da suka tuba zuwa gonaki, tsohon Janar ya shawarci FG
A gefe guda, tsohon shugaban horaswa da ayyuka a Hedikwatar rundunar Soji da ke Abuja, Birgediya Janar John Sura (mai ritaya), a ranar Juma'a, ya shawarci Gwamnatin Tarayya da ta tura 'yan ta'addan Boko Haram sama da 1,000 da suka tuba zuwa gona.
A cewarsa, ya kamata a yi amfani da su wajen aikin gona da suka hana ‘yan gudun hijira da sauran ‘yan Najeriya yi.
Ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai taken 'Ku dauki 'yan ta'addan Boko Haram da suka tuba a matsayin fursunonin yaki', jaridar Punch ta ruwaito.
Asali: Legit.ng