Take hakkin dan Adam: UN ta aiko wa Najeriya wasika, ta bukaci bayanai 5 game da Kanu
- Majalisar dinkin duniya ta aiko wa da Najeriya wasika domin neman karin bayani game da kamen shugaban IPOB, Nnamdi Kanu
- Wasikar ta kunshi zargin azabtarwa da kuma cutarwa da Kanu ke fuskanta a hannun hukumar DSS tun bayan da aka mika shi hannunsu
- UN ta bukaci sanin ta yadda aka damke Kanu a Kenya kuma ya bayyana a Najeriya inda ta ce akwai zargin take hakkin dan Adam a lamarin
Majalisar dinkin duniya ta bukaci gwamnatiin tarayya da ta samar da wasu bayanai kan shugaban kungiyar 'yan awaren IPOB, Mazi Nnamdi Kanu.
Jerin tambayoyin suna kunshe ne a wata takarda da majalisar dinkin duniyan ta aiko wa da gwamnatin tarayya mai kwanan wata 27 ga watan Augusta.
Kamar yadda majalisar dinkin duniyan ta ce, ta samu rahotanni kan zargin take hakkin dan Adam da gwamnatin tarayya ke wa Kanu.
"Duk da ba mu yanke hukunci da wadannan zargin ba, muna son bayyana damuwarmu kan bata da Nnamdi Kanu ya yi daga ranar 19 ga Yuni har zuwa bayyanarsa a gaban babbar kotun tarayya a ranar 29 ga watan Yuni a Najeriya," takardar tace.
"An sake sanar mana zargin gallazawa da kuma cutar da Kanu da ake yi yayin da ya ke hannun hukumar DSS a Najeriya. Idan aka tabbatar da wadannan zargin, tabbas an take masa hakkinsa na dan Adam, hakkin 'yanci, cutarwa da kuma azabtarw,a" takardar ta sanar.
Sun bukaci gwamnatin tarayya da ta samar da wasu bayanai uku kan Kanu da suka hada da:
1. Samar da bayani kan lafiyar Kanu a halin yanzu ko kuma matakan da aka dauka domin guje wa illata rayuwarsa da nagartarsa da kuma damar da aka bashi wurin samun lafiya.
2. Samar da bayani dalla-dalla kan halin da Kanu ya ke ciki yayin da aka kama shi tare da saka karfi wurin mika shi ga hukumomin Najeriya daga Nairobi zuwa Abuja. A bada takardar kotu da ta bada damar aikata hakan.
3. Samar da bayani kan ko an yi bincike a kan batan Kanu cikin kwanaki goma ko kuma an tuhumi wadanda suka assasa batansa.
4. Samar da bayani idan akwai, na hadurran da ke kunshe da azabtarwa, mugunta da ladabtar da Kanu da hukumonin Kenya suka yi yayin tsare shi kafin a dawo da shi Najeriya.
5. Samar da bayani kan matakan da aka dauke wurin bincikar zargin cutarwa da azabtarwar da aka yi wa Kanu yayin da ya ke tsare a Kenya kuma da hukuncin da aka yi wa masu hannu a ciki.
Sai dai, wakilan najeriya da ke ofishin majalisar dinkin duniya da sauran kungiyoyi da ke Geneva sun tabbatar da samun wasikar a ranar 17 ga watan Satumba.
Garba Shehu: Shari'ar Nnamdi Kanu za ta kawo karshen ta'addancin IPOB
A wani labari na daban, Malam Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa, ya ce shari'ar Nnamdi Kanu za ta kawo karshen ta'addancin kungiyar 'yan awaren Indigenous People of Biafra (IPOB).
Ya sanar da hakan ne yayin martani kan caccaka mai zafin da wata jaridar London, The Economist ta yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari, Daily Trust ta wallafa.
Jaridar ta caccaki gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari inda ta ce mulkinsa ya gaza shawo kan rashawa, Daily Trust ta ruwaito.
Asali: Legit.ng