Lauyoyin Igbo sun bukaci a shigar dasu cikin karar da dattawan Arewa suka kai kotu na korar Igbo daga Najeriya

Lauyoyin Igbo sun bukaci a shigar dasu cikin karar da dattawan Arewa suka kai kotu na korar Igbo daga Najeriya

  • Lauyoyi daga kabilar Igbo sun ce lallai a shigar da su cikin karar da dattawan Arewa suka kai kotu
  • Dattawan Arewa dai sunce maimakon asarar rayuka da dukiya, kawai a cire yankin kudu masi yamma daga Najeriya
  • Daga cikin wadanda aka shigar kara akwai shugaban majalisar dattawa da Ministar Shari'ar Najeriya

Abuja - Lauyoyin yankin kabilar Igbo sun bukacimika bukatar babbar kotun tarayya dake Abuja na bukatar a shigar da su cikin karar da dattawan Arewa suka shigar kotun na korar yankin Kudu maso gabas daga Najeriya.

Lauyoyin karkashin jagoranicin Chief Chuks Muoma (SAN), Ukpai Ukairo, Ebere Uzoatu da Obi Emuka sun bukaci kotu cewa a sanyasu cikin karar domin su kare muradin yankinsu, rahoton Guardian.

A bukatar da suka shiga ta hannun Victor Onweremadu ranar Litnin a Abuja, sun ce lallai sun da ta cewa kan karar da dattawan Arewa suka shigar saboda hakan na da muhimmanci ga rayuwar al'ummar Igbo.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari za ta sake komawa kotu da Sanatan da ya fito daga gidan yari a 2020

Kungiyoyin Arewa sun shigar da kara kotu a cire yankin Igbo daga Najeriya

Gamayyar Kungiyoyin Arewacin Najeriya ta nemi babban kotun tarayya dake Abuja ta roki 'yan majalisu su cire yankin kudu maso gabas daga Najeriya kafin kammala gyaran fuskan kundin tsarin mulkin Najeriya.

Nastura Ashir Shariff, Balarabe Rufa’I, Abdul-Aziz Sulaiman da Aminu Adam sun shigar da batun kotu tare da bayyana cewa, hakan zai taimaka wajen rage faruwar rikice-rikice da zubar da jinane a daga 'yan awaren yankin.

Sun yi ikirarin cewa ba sa son a maimaita yakin basasar da aka yi a Najeriya tsakanin 1967 zuwa 1970 wanda ya jawo asarar rayuka da dukiyoyin al’ummar kasar da yawansu ya kai biliyoyin Naira.

Lauyoyin Igbo sun bukaci a shigar dasu cikin karar da dattawan Arewa suka kai kotu na korar Igbo daga Najeriya
Lauyoyin Igbo sun bukaci a shigar dasu cikin karar da dattawan Arewa suka kai kotu na korar Igbo daga Najeriya Hoto: IPOB
Asali: Getty Images

Su wa aka shigar kara?

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa sun tafi kotu, sun bukaci a raba Najeriya, a ware 'yan wani yankin kudu

Wadanda gammayar ta kai kara kotu sun hada da Antoni Janar na kasa, Abubakar Malami; Shugaban majalisar dattawa, shugaban majalisar wakilai, da kuma majalisar dokokin tarayya gaba daya.

Lauyoyin yankin kuwa sun ce lallai akwai bukatar a hada da su saboda babu dan kabilarsu ko guda kuma suna da ta cewa ciki.

An dage zaman sauraron karar zuwa ranar 1 ga Nuwamba, 2021.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng