Sau biyar kenan, an ceci wani mutumin da ke kokarin kashe kansa a Abuja

Sau biyar kenan, an ceci wani mutumin da ke kokarin kashe kansa a Abuja

  • Karo na biyar, Jami'an gwamnati a Abuja sun ceci mutumin da
  • ke kokarin daukar rayuwarsa da kansa
  • Mutumin wanda tsohon injiniya ne ya bayyana cewa rayuwa tayi masa kunci ga kuma matsanancin yunwa
  • A cewarsa, gida daya da ya mallaka a Abuja gwamnati ta rusa kuma yanzu ba shi da wajen zama gaba daya

Abuja - Sakatariyar jin dadin al'umma na hukumar birnin tarayya Abuja, ta ceci wani dattijo dan shekara 56 a duniya wanda ke kokarin daukar ransa saboda kuncin rayuwar.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta bayyana cewa mutumin wanda tsohon Injiniya ne karo na biyar kenan da yayi kokarin hallaka kansa.

Mukaddashin Diraktan jin dadin al'umma na ma'aikatar, Sani Amar, ya bayyana hakan a hirarsa da manema labarai ranar Talata a Abuja.

Mr Amar ya yi bayanin cewa ofishinsa ta samu labarin ne ta bakin wani ma'aikacinsa.

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun kai hari masallaci, sun bindige masallata a jihar Neja

A cewarsa:

"Mutumin ya dade yana kokarin kashe kansa, ya yi amfani da leda wajen rufe fuskarsa don kada mutane su gane."

Diraktan ya bayyana cewa zasu kai shi asibiti domin duba lafiyarsa da kuma bincike.

Hakazalika ya bayyana cewa dan jihar Rivers ne.

Yace:

"Mun tuntubi ofishin gwamnan jihar Rivers dake Abuja saboda a bibiyi iyalansa."

Sau biyar kenan, an ceci wani mutumin da ke kokarin kashe kansa a Abuja
Sau biyar kenan, an ceci wani mutumin da ke kokarin kashe kansa a Abuja Hoto: DN
Asali: Facebook

Me yasa yake kokarin kashe kansa?

Diraktan ya ci gaba da cewa mutumin na kokarin hallaka kansa ne saboda kuncin rayuwa, abubawa sun kare masa, ba shi da gidan kansa kuma ba shi da inda zai tura kansa.

A cewarsa:

"Da safen nan, ya fada min cewa kwanansa hudu rabon da yaci abinci. Yana jin yunwa kuma ba shi da lafiya."

Kara karanta wannan

Tsananin kishi ya sa saurayi ture budurwarsa har lahira a Bauchi

Hirar da aka yi da mutumin

Mutumin, wanda babban Injiniyan ruwa ne mai ritaya ya yi tsokaci kan dalilin da yasa yake kokarin hallaka kansa kan babban titin Mabushi, wajen gadar Jabi Lake.

Karanta abin da ya fada:

"Na yanke shawarar kashe kaina saboda abubuwa sun kare min, babu gida. Dan gidan da na mallaka a Kabusa an rusa."
"Ba nida wajen zuwa. Gashi babu lafiya kuma ba zan iya biyan kudin asibiti ba."
"Wani mutum ya kai ni wata tashar rediyo don ganin idan zasu taimaka min. Da muka isa wajen aka ce masa ya kawo rahoto daga wajen yan sanda, har yanzu ban sake ganinsa ba."

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng