Abin da Shugaba Buhari ya fada mani game da Sunday Igboho a Aso Villa inji Oonin Ife

Abin da Shugaba Buhari ya fada mani game da Sunday Igboho a Aso Villa inji Oonin Ife

  • Adeyeye Ogunwusi Ojaja yace Sunday Igboho bai ji maganar Sarakuna ba
  • Sarkin na kasar Ife ya zargi ‘yan siyasa da yaudarar ‘dan gwagwarmayar
  • Igboho bai ji shawarar da manya suka ba shi, a karshe aka rufe shi a Benin

Ife - Mai martaba Ooni na kasar Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi Ojaja II ya nuna takaicinsa a kan yadda aka tsare Sunday Adeyemo (Igboho) a kasar Benin.

Jaridar This Day ta kawo labarin hirar da Sarki Oba Adeyeye Ogunwusi Ojaja II ya yi da ‘yan jarida.

Oba Adeyeye Ogunwusi yace sau biyu Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Igboho yana watsi da shawarwarin da sarakunan yarbawa suka je suka ba shi.

Basaraken yace da suka hadu da shugaba Buhari kan lamarin Sunday Igboho, sai shugaban kasar yace ya kamata Igboho ya natsu, ya kwantar da hankalinsa.

Kara karanta wannan

Gwamna ya gwangwaje Mbaka da N30m, doya 200 da buhun shinkafa 100 don ya daina sukar Buhari

“Mutane da dama sun ba shi mummunar shawara... sai ya saurare su.”

Rahoton yace shugaban Najeriyar ya kuma yi kira ga sarakunan kudu maso yamma shawara su ja-kunnen Igboho kan yin abubuwan da za su sabawa dokar kasa.

Oonin Ife
Ooni Of Ife ya ziyarci Buhari a Abuja Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Na ziyarci Buhari a kan batunsa, na fada masa Igboho yaronmu ne, yace mani ya kamata shi (Igboho) ya natsu, ya kwantar da hankalinsa.” – Oba Ogunwusi II.
“Buhari ya fada mani Sarakunan Yarbawa su ja masa kunne. Bayan na bar fadar shugaban kasa, na tara Sarakunanmu suka ba shi shawara, amma bai ji ba.”

Ba a iya fada da Gwamnati

A cewar Sarkin na kasar Ife, Igboho yana da dalilin fafutukar da ya dauko, amma yace ya kamata ya yi amfani da lalama da sulhu wajen cin ma manufar ta sa.

Sarki Adeyeye Ogunwusi yana ganin ‘yan siyasa ne suka yi amfani da Igboho, suka yaudare shi, amma duk da haka akwai bukatar Sarakuna su mara masa baya.

Kara karanta wannan

Rarara ya bada shawarar a kyale Buhari ya yi ta mulki har zuwa shekarar 2027 ko 2028

Zuwa yanzu Sarkin na kasar Yarbawa yace ya yafewa Sunday Igboho, kuma ya na kokarin ganin an fito da shi daga inda yake tsare a kasar Jamhuriyyar Benin.

A hirar da aka yi da shi, Oba yace ya kamata sauran ‘yan gwargwamaya masu fafutuka a yankin kudancin kasar su rungumi lalama, domin ba a yakar gwamnati.

Za a daina biyan tallafin fetur a 2023

A jiya aka ji cewa nan da shekarar 2022, gwamnatin tarayya za ta cire hannu daga tallafin fetur. Tallafin man zai ci wa Najeriya Naira tiriliyan 2.9 a shekarar nan.

Ministar tattalin arziki da kasafin kudi ta kasa, Zainab Ahmed tace babu abin da gwamnatin Buhari ta ware domin tallafi bayan Yunin 2022 a kasafin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng