Sultan ya yi wa direban da ya mayar da N500,000 da aka manta a kekensa kyautar kudi mai tsoka

Sultan ya yi wa direban da ya mayar da N500,000 da aka manta a kekensa kyautar kudi mai tsoka

  • Sultan ya yi wa direban da ya mayar da N500,000 da fasinja ya manta a kekensa kyautar kudi
  • Direban mai suna Malam Tulu ya samu kwatankwacin kudin da ya mayar a matsayin kyauta daga Sultan
  • Ya yi hakan ne sakamakon dadi da ya ji kan gaskiya da amana da dan adaidaitan ya nuna duk da kasancewarsa mabukaci

Masu iya magana sun ce alkhairi danko ce, hakan ce ta kasance ga wani bawan Allah mai suna Malam Tulu wanda ya kasance matukin keken adaidaita sahu.

Da farko dai mun ji cewa Malam Tulu ya tsinci kudi da wasu 'yan kasuwa suka manta a cikin adaidaitarsa har kimanin N500,000.

Sultan ya yi wa direban da ya mayar da N500,000 da aka manta a kekensa kyautar kudi mai tsoka
Sultan ya yi wa direban da ya mayar da N500,000 da aka manta a kekensa kyautar kudi mai tsoka Hoto: BBC News Pidgin
Asali: Facebook

Sai dai kuma bai yi kasa a gwiwa ba wajen mayarwa da ‘yan kasuwar kudinsu, inda aka yi masa kyautar N5000 a matsayin tukwici.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Basirar fasihin makaho ta burge Ganduje, ya bashi aiki nan take

A yanzu kuma, labari da muke samu daga sashin BBC Pidgin, ya nuna cewa Sultan ya ji dadin wannan gaskiya da Malam Tulu ya nuna inda yayi masa kyautar kudi mai tsoka.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A bisa ga rahoton da shashin labaran ya yada a Facebook, Sultan ya bai wa mai keken kwatankwacin kudin da ya tsinta wato naira dubu dari biyar.

Ya rubuta a shafin nasa:

“Yana da kyau mutum ya zamo mai gaskiya!
“Wannan mai keken adaidaita sahun ya mayar da N500,000 da fasinja ya manta a kekensa.
“Yanzu direban ya samu kwatankwacin kudin daga wajen Sultan a matsayin kyauta.
“Don haka wannan dan takaitaccen labarin ya karfafa maka gwiwa a yau.”

Direba ya mayar wa 'yan kasuwa N500,000 da suka manta da ita a Kekensa

A baya mun kawo cewa, wani matukin Keke ta haya mai suna Mallam Tulu, ya mayar da kudi har N500,000 zuwa ga wasu 'yan kasuwa bayan sun manta da shi a abun hawansa a Jos, jihar Filato.

Kara karanta wannan

Kano: Mai kwacen waya ya halaka tela mai shekaru 30 a adaidaita sahu

Kamar yadda wani Bello Lukman na Unity FM Jos ya wallafa a shafinsa na Facebook, 'yan kasuwan su na kan hanyarsu ta zuwa siyan shanu a yankin Yanshanu da ke Jos a ranar Asabar, 16 Oktoba yayin da suka manta da kudin.

"Allah ya albarkaci Mallam Tulu, matukin Keke wanda ya dawo wa da fasinjojin 'yan kasuwa kudi har dubu dari biyar da suka manta da su a Kekensa a Jos," ya ce.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng