'Yan Boko Haram sun kai sabon hari Yobe, sun sha ruwan wuta a hannun sojojin Najeriya
- Mayakan Boko Haram sun kai hari wani yankin jihar Yobe, sun hadu da aikin sojojin Najeriya
- Rahoto ya bayyana cewa, an hallaka da dama tare da rauna 'yan ta'addan na Boko Haram
- A bangare guda, an ce wasu daga cikin jaruman sojojin Najeriya sun ji munanan raunuka a harin
Yobe- Mayakan Boko Haram, a ranar Asabar 24 ga watan Oktoba, sun kai hari kan sansanin sojoji da ke kauyen Katarko da ke karamar hukumar Gujba ta jihar Yobe.
Wasu majiyoyi sun shaidawa TheCable cewa maharan sun shiga kauyen Katarko ne a cikin manyan motocin yaki guda 10 sannan suka kai hari kan sojoji.
An ce sun fafata da jami'an tsaro da ke sansanin a musayar wuta da suka yi.
Sojojin kasa na Najeriya, wadanda suka dakile harin, tare da ruguden wuta daga sama da rundunar sojin saman Najeriya (NAF) ta yi, an ce sun kashe da yawa daga cikin maharan.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sai dai, ba a tabbatar da adadin wadanda suka mutu ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.
An kuma ce sojoji uku sun jikkata a harin.
A cewar majiyar:
“Sojoji biyu zuwa uku sun ji rauni kuma an kai su asibiti a Damaturu don yi musu magani."
“Ana kuma fargabar da yawa daga cikin 'yan Boko Haram sun mutu. Sojojin sama da taimakon na sama sun fatattake su.”
Al’ummomin yankin Yobe na ci gaba da fuskantar hare-hare da yawa daga masu tayar da kayar baya a cikin ‘yan shekarun nan.
Sabon hari: 'Yan bindiga sun hari ofishin 'yan sanda, sun kashe 3, an hallaka dan bindiga 1
The Nation ta ruwaito cewa, an harbe jami’ai uku a cikin ofishin ‘yan sanda da ke Unwana, karamar hukumar Afikpo ta Arewa a jihar Ebonyi.
Wata majiya ta shaida wa Daily Trust cewa jami’an da suka mutu akwai kwanstabul da sifetoci biyu.
Wani mazaunin Uwana, wanda bai so a ambaci sunansa ba, ya ce 'yan bindigar sun rufe fuska.
Sojoji na gina rugar Fulani a kudu: Rundunar soji ta yi martani kan jita-jita
A wani labarin, rundunar sojin Najeriya ta karyata jita-jitar da ke yawo mai cewa, a halin yanzu wata runduna na gina matsugunar Fulani a yankin kudu maso gabashin Najeriya.
Jita-jitar da ake yadawa ta ce, runduna ta 82 ta sojin Najeriya tana aikin gina rugar Fulani a tsakanin Ochima da Affa a cikin Igbo-Etiti da Udi na jihar Enugu.
A cikin wata sanarwar da Legit.ng Hausa ta samu a ranar Laraba 13 ga watan Oktoba dauke da sa hannun Manjo Abubakar Abdullahi, Mukaddashin Mataimakin Daraktan Hulda da Jama'a na Rundunar, rundunar sojin Najeriya ta watsi da batun.
Asali: Legit.ng