Kano: Mai kwacen waya ya halaka tela mai shekaru 30 a adaidaita sahu
- Barayin waya a kwaryar birnin Kano sun soka wa matashin tela wuka a cikin adaidaita sahu kan hanyarsa ta zuwa ta'aziyya
- Mummunan lamarin ya auku a ranar Juma'a yayin da barayin suka bukaci wayarsa amma ya wurga ta waje kan titi
- 'Yan sanda sun kai dauki inda suka dinga kama mutane wurin titin Zungeru bayan barayin sun soka masa wuka a cinya tare da tserewa
Kano - Wani mai kwacen waya a jihar Kano ya soka wa matashin tela mai shekaru talatin wuka mai suna Abdullahi Bala da ke karamar hukumar Fagge ta jihar.
Daily Trust ta ruwaito cewa, an kashe shi a ranar Juma'a wurin titin Zungeru zuwa Festing da ke birnin Kano yayin da ya ke kan hanyarsa ta zuwa ta'aziyya bayan rufe shagonsa da yayi.
Wani dan uwan mamacin mai suna Yazid Ali Fagge, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga Daily Trust inda ya yi bayanin cewa an soka wa marigayi Bala wuka ne wurin karfe 6:45 na yammacin Juma'a.
Ya ce, "Ya hau adaidaita sahu a kan hanyarsa ta zuwa ta'aziyya unguwar Birgade, bai san cewa direban da fasinjoji da ke ciki barayin waya ba ne.
"Sun ce ya basu wayarsa, amma sai ya wurga ta waje domin neman daukin jama'a kan abinda ke faruwa. Daga nan ne suka soka masa wuka a cinyarsa kuma suka tsere.
“An yi hanzarin kiran 'yan sanda kuma daga nan suka fara kamen 'yan adaidaita sahu, Sai dai har yanzu ba a gano wadanda suka yi mugun aikin ba.
"'Yan sanda ne suka kai shi asibitin kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano kuma mu kan mu 'yan uwansa sai a ranar Asabar 'yan sanda suka sanar da mu rasuwarsa. Yanzu haka daga wurin jana'izarsa muke wacce aka yi da safen nan," Fagge yace.
A yayin tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, Abdullahi Kiyawa ya tabbatar da cewa an cafke mutum 2 da ke da alaka da kisan kan kuma za a gurfanar da su a gaban kuliya.
Kamar yadda yace, ana cigaba da bincike kan al'amarin domin kamo sauran wadanda ke da hannu a ciki.
Kano: Muhuyi ya bukaci babbar kotu da ta haramtawa 'yan sanda kama shi
A wani labari na daban, dakataccen shugaban hukumar sauraron korafin jama'a da yaki da rashawa na jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimingado, ya bukaci wata babbar kotun tarayya da ke Kano da ta hana 'yan sanda kama shi.
Sai dai kuma, kotu da ke samun shugabancin Mai shari'a Jane Inyang, a ranar Laraba ta umarci wadanda ake kara, da suka hada da 'yan sanda tare da kakakin majalisar jihar da su bayyana a gaban ta.
Daily Trust ta ruwaito cewa, kotun ta na son jin dalilin da zai sa kada ta karba bukatar tsohon shugaban hukumar yaki da rashawan na jihar.
Asali: Legit.ng