Cikin mako ɗaya, Miyagun yan bindiga sun hallaka Sarakuna biyu da wasu mutum 45 a Najeriya
- Aƙalla mutum 47 tsagurun yan bindiga suka hallaka a makon da ya gabata, cikinsu har da sarakuna biyu
- Rahotanni sun nuna cewa adadin fararan hula da mahara suka kashe ya linka biyu idan aka kwatanta da na wancan makon
- Sai dai a ɗaya ɓangaren kuma an samu saukin yawaitar hare-hare, amma harin Sokoto shine ya fi muni
Abuja - Matsalar tsaro ta ƙaru a Najeriya yayin da adadin mutanen da aka kashe ya ƙaru a wannan makon, idan aka kwatanta da na makon da ya shuɗe kafin shi.
Aƙalla yan Najeriya 47 ne suka rasa rayukansu a hare-haren yan bindiga a faɗin Najeriya makon da ya gabata (17-23 ga watan Oktoba).
Jaridar Premium Times ce ta haɗa adadin daga rahotannin da kafafen watsa labarai suka buga, babu wanda ba'a rahoto ba a ciki.
Hakanan kuma adadin fararen hula da aka kashe ɗin ya karu da kashi 50 a wannan makon idan aka kwatanta da mutum 31 da aka kashe makon da ya shuɗe kafin shi, cikinsu akwai jami'an tsaro 10.
Yayin da adadin waɗanda mahara suka kashe ya ƙaru, a ɗaya bangaren yawan hare-haren ya ragu, inda makon da ya gabata hari 4 kacal aka kai.
Sama da kashi 90 na kisan da aka yi makon da ya gabata ya faru ne a yankunan arewa ta yamma, yayin da sauran ya auku a sauran sassan Najeriya.
An hallaka mutum 43 a Sokoto
Aƙalla mutum 43 aka ruwaito maharan sun hallaka yayin da suka farmaki masu siya da masu siyarwa a kasuwar Goronyo, jihar Sokoto.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kwashe fiye da awanni 2 suna harbi kan mai uwa da wabi, ba tare da samun martani daga jami'an tsaro ba saboda babu damar sanar dasu sakamakon datse sabis.
Yan Najeriya da dama sun yi Allah wadai da wannan mummunan harin, inda shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin ragargazan yan ta'addan da sauran ƙungiyoyinsu dake yankin.
Sarakuna biyu a jihar Imo
Mutane sun shiga yanayin tashin hankali a jihar Imo, yayin da wasu tsagerun yan bindiga suka buɗe wuta kan sarakunan gargajiya dake gudanar da taro, mutum 2 suka mutu.
Rahotanni sun bayyana cewa sarakunan suna gudanar da taron masu faɗa aji na yankin Nnenasa, hedkwatar ƙaramar hukumar Njaba, lokacin da maharan suka kutso.
Mafi yawan sarakunan da suka halarci taron sun samu raunuka kala daban-daban yayin harin.
Mutum ɗaya a Kwara
Hukumar yan sanda a jihar Kwara da sanar da kashe mutum ɗaya mai suna, Sina Babarinde.
Kakakin yan sandan jihar, Okasanmi Ajayi, wanda ya tabbatar da kisan ranar Litinin, yace an kashe mutumin ne yayin da suke tsaka da ibada a coci.
A cewarsa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7:00 na safe yayin da ake gudanar da ibadun cocin RCCG.
Soja ɗaya a Imo
Hakanan kuma an shiga tashin hankali a karamar hukumar Ohaji Egbema, jihar Imo, yayin da sojoji suka yi arangama da matasa ranar Laraba.
Rahoto ya tabbatar da cewa kwantan bauna suka yi wa sojan, inda suka kashe shi kuma suka yi awon gaba da bindigarsa.
Yayin ɗaukar fansa, Sojojin sun mamaye yankin yayin da suka ƙona gidaje, wanda ya jawo arangama tsakaninsu da matasa.
A wani labarin kuma kun ji cewa Wani basarake a jihar Katsina ya koka matuƙa kan yadda yan bindiga suka hana mutane sakat a jihar
Basaraken yace a halin yanzun yan ta'addan sun hana mutane sakat, ta hanyar kashe su da kuma hana su zuwa gonakinsu.
A cewarsa yanzun yan bindiga ne suke kwashe abincin da mutane suka noma a gonaki.
Asali: Legit.ng