Mun nemi gwamnatin tarayya ta dawo da hanyoyin sadarwa a jihar Sokoto, Tambuwal
- Gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, yace gwamnatinsa ta nemi hukumar sadarwa ta ƙasa NCC ta ɗage matakin datse sabis
- Gwamnan yace jami'an tsaro a jihar sun koka cewa aikin su na musu wahala saboda rashin sadarwa
- Tun a watan Satumba ne hukumar sadarwa ta ƙasa ta datse sabis na layukan sadarwa a ƙananan hukumomi 14 na jihar Sokoto
Sokoto - Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto, ya bayyana cewa tuni ya aike da wasikar neman gwamnatin tarayya ta dawo da hanyoyin sadarwa a jihar.
Gwmanan ya faɗi haka ne a wata sanarwa da kakakinsa, Muhammad Bello, ya fitar ranar Asabar.
BBC Hausa ta ruwaito Tambuwal yace ya tura takardar neman a ɗage matakin datse hanyoyin sadarwa da ka ƙaƙaɓa a wasu yankunan jihar.
Da dumi: Uwar jam'iyya ta watsawa Shekarau kasa a ido, ta ce zaben Abdulahi Abbas kadai ne zaben da ta sani
Meyasa gwamnan ya nemi a ɗage matakin?
A sanarwan, gwamna, mai magana da yawun gwamnan yace:
"Gwamana yace ya bukaci a dawo da hanyoyin sadarwan ne saboda jami'an tsaro sun ce rashin sadarwa na kawo musu naƙasu a gudanar da ayyukansu."
A cewar sanarwan, gwamna Tambuwal ya faɗi haka ne yayin da ya karbi bakuncin gwamnan jihar Borno, Babagana Umaru Zulum.
Gwana Zulum ya kai wannan ziyara ne domin jajantawa gwamnatin jihar da kuma al'umma bisa mummunan harin da aka kai kasuwar Goronyo.
Yaushe aka datse hanyoyin sadarwa a Sokoto?
Idan baku manta ba, tun a watan Satumba, hukumar sadarwa ta ƙasa (NCC) ta datse sabis na layukan salula a kananan hukumomi 14 na jihar Sokoto.
Hukumar ta fara da katse sadarwa a jihar Zamfara, sannan sai jihar Katsina ta biyo, kafin daga bayan jihar Kaduna ta ɗauki irin wannan matakin.
A wani labarin kuma Sama da mutum 500 sun mutu, wasu sama da 20,000 sun kamu a Jigawa
Rahoto ya nuna cewa aƙalla mutum 500 ne suka rasa rayuwarsu tun bayan ɓarkewar kwalara a jihar Jigawa.
Hakanan kuma cikin watanni hudu da suka gabata bayan ɓarkewar cutar, aƙalla mutum 20,000 ne suka harbu da ita.
Asali: Legit.ng