Harin Oyo: Hukumar Gidajen Yari ta bayyana adadin Fursunonin da suka gudu da wadanda aka damko
- Hukumar gidajen gyara hali tayi magana kan harin da yan bindiga suka kai gidanta dake Oyo
- Daga cikin wadanda suka gudu, an samu nasarar ceto kashi daya cikin uku
- Kwantrola Janar na hukumar ya lashi takobin damko sauran
Ibadan - Hukumar gidajen gyara hali ta jihar Oyo, ta bayyana cewa Fursunoni 837 ne suka arce daga gidan yarin Abolongo sakamakon harin da yan bindiga suka kai daren Juma'a.
Kakakin hukumar, Olanrewaju Anjorin, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Asabar, a Ibadan, rahoton NAN.
Olanrewaju yace dukkan Fursunonin dake sauraron gurfana gaban kotu 837 ne suka arce amma wadanda tuni aka yanke musu hukunci na nan ba'a shiga inda aka ajiyesu ba.
Yace kawo yanzu an damko mutum 262 cikin wadanda suka gudu, yayinda ake neman 575.
Me ya faru?
A cewarsa:
"Yan bindigan sun dira gidan yarin da manyan makamai kuma bayan artabu da jami'an tsaro dake gadi, sun samu nasarar shiga cikin kuma sukayi amfani da nakiya wajen fasa bangon."
"Sun fitar da dukkan wadanda ake tsare, amma basu samu shiga inda Fursunonin da aka yankewa hukunci suke ba."
"Kawo yanzu an damko wadanda suka gudu mutum 262, saura 575 da suka gudu."
Adadin mutum nawa gidan yarin ke dauka?
Ya kara da cewa an gina gidan yarin ne a 2007 kuma asali mutum 160 zai dauka, amma yanzu mutane 907 ke zama.
"Daga cikinsu, mutum 837 na sauraran gurfana a kotu, mutum 64 kadai aka yankewa hukunci," Anjorin yace.
Kalli bidiyon wadanda aka damko (Bidiyon TVC):
Mun kawo muku rahoton cewa yan bindiga sun kai hari gidan yarin dake Abolongo, a jihar Oyo ranar Jumu'a da daddare.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kutsa cikin gidan yarin, sannan suka saki dukkan fursunonin dake ciki.
Miyagun yan bindigan sun fasa gidan yari ne da tsakar dare, inda suka yi amfani da gurneti wajen tilasta samun damar shiga harabar gidan gyaran halin.
Asali: Legit.ng