Barkewar cutar kwalara: Sama da mutum 500 sun mutu, wasu sama da 20,000 sun kamu a Jigawa

Barkewar cutar kwalara: Sama da mutum 500 sun mutu, wasu sama da 20,000 sun kamu a Jigawa

  • Rahoto ya nuna cewa aƙalla mutum 500 ne suka rasa rayuwarsu tun bayan ɓarkewar kwalara a jihar Jigawa
  • Hakanan kuma cikin watanni hudu da suka gabata bayan ɓarkewar cutar, aƙalla mutum 20,000 ne suka harbu da ita
  • Gwamnatin jihar ta bayyana cewa tana iya bakin kokarinta wajen dakile yaɗuwar cutar a faɗin jihar

Jigawa - Sama da mutum 500 sun riga mu gidan gaskiya cikin watanni huɗu bayan barkewar cutar kwalara a jihar Jigawa, arewa maso yamma.

Channels tv ta ruwaito cewa duk da matakan da hukumomi ke ɗauka cutar ta kama mutane sama da 20,000 zuwa yanzu a faɗin jihar.

Kananan hukumomi 22 cikin 27 dake jihar Jigawa ne suke fama da annobar cutar ta kwalara tun bayan ɓarkewarta.

Jihar Jigawa
Barkewar cutar kwalara: Sama da mutum 500 sun mutu, wasu sama da 20,000 sun kamu a Jigawa Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Babban birnin jihar, Dutse, da kuma ƙananan hukumomin Birnin Kudu da Haɗeija, sune wuraren da cutar ta fi yin illa.

Kara karanta wannan

EndSARS: Babu wanda sojoji suka kashe lokacin zanga-zanga, Gwamnatin Tarayya

Wane matakai gwamnatin jihar ta ɗauka?

Sakataren hukumar kula da lafiya a matakin farko na jihar, Kabir Ibrahim, ya tabbatarwa al'ummar jihar cewa gwamnati ta ɗauki matakan daƙile yaɗuwar cutar.

Ya yi wannan furucin ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Dutse, yace an yi wa mutum 720 rigakafin cutar a garuruwa uku da tafi yin illa.

A jawabinsa yace:

"Gwamnatin tarayya ta aiko mana da rigakafi miliyan 1.4m. Tun daga ɗan shekara ɗaya zuwa shekarun samartaka za'a musu rigakafin."
"Amma a halin yanzun mun maida hankali kan waɗannan wuraren uku, kowane mutum ɗaya za'a masa sau biyu, mako hudu tsakani."

Me gwamnati take bukata daga mutane?

Daga ƙarshe ya roki mutanen jihar da su baiwa hukumomi haɗin kai domin cimma kudirin dakile yaɗuwar cutar.

Kara karanta wannan

Yadda yan bindiga ke sako mutanen da suka kama ba tare da biyan kudin fansa ba a Zamfara

A cewar hukumar lafiya ta duniya (WHO) a kowace shekara ana samun mutum miliyan 1.3m zuwa 4m dake kamuwa da cutar.

Ya yin da a cikin wannan adadi ana samun mutum 21,000 zuwa 143,000 da cutar ke sanadiyyar mutuwarsu.

A wani labarin kuma Wani babban malami ya ɗirkawa budurwa cikin shege daga zuwa neman addu'a

Wani limamin coci a jihar Ondo, ya shiga hannun yan sanda bisa zarginsa da yi wa wata budurwa ciki daga zuwa neman addu'a.

Faston dai ya amsa laifinsa da farko, amma daga baya ya musanta tuhumar da ake masa, amma ya amince zai ɗauki nauyin mai cikin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: