Borno: Zulum ya sanar da ranar da za a rufe dukkanin sansanonin ƴan gudun hijira a Maiduguri
- Daga ranar 31 ga watan Disamba mai zuwa, gwamnatin jihar Borno za ta rufe duk wasu sansanin ‘yan gudun hijira da ke Maiduguri
- Gwamnan jihar, Babagana Zulum ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a yayin tattaunawa da manema labaran cikin gidan gwamnati a Abuja
- Ya sanar da hakan ne bayan kammala taro da shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce sun dauki matakin ne saboda ci gaban da aka samu na tsaro a jihar
Borno - Gwamnatin jihar Borno ta ce za ta rufe duk wasu sansanin ‘yan gudun hijira da ke cikin babban birnin jihar, Maiduguri zuwa ranar 31 ga watan Disamba.
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, Babagana Zulum ne ya sanar da hakan a ranar Juma’a yayin zantawa da manema labaran cikin gidan gwamnati.
Ya sanar da hakan ne bayan kammala wani taro da shugaban kasa Muhammadu Buhari a Abuja, bisa ruwayar The Cable.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewarsa, sun yanke wannan shawarar ne bayan ganin yadda harkokin tsaro su ka gyaru a halin yanzu a cikin jihar.
A cewar sa, gwamnatin za ta tashi ‘yan gudun hijirar ne don su koma gidajen su da su ka saba zama a ciki.
Ya ce:
“Na zo sanar da shugaban kasa ne yadda gwamnatin jihar Borno ta ke kokarin ganin ta mayar da ‘yan gudun hijira gidajen su.
“A halin da ake ciki, gwamnatin jihar Borno ta fara yin duk wasu shirye-shirye na tabbatar da rufe sansanayen ‘yan gudun hijira da ke Maiduguri zuwa ko kuma kafin 31 ga watan Disamba.”
Zulum ya ce gwamnatin jihar Borno ta hada kai da ma’aikatar jin kai
A cewar gwamnan, jihar ta hada kai da ma’aikatar jin kai ta kasa don yin duk wasu shirye-shiryen tabbatar da maido da duk wadanda ke Nijar da Kamaru
Sannan zuwa ranar 27 ga watan Nuwamba, gwamnatin jihar Borno za ta sauya wa ‘yan gudun hijira da ke zama a Nijar wuri zuwa Malumfatari, wata karamar hukuma a Borno, inda yanzu babu mutane sosai saboda ta’addanci.
Zulum ya yaba wa jami’an tsaro akan kokarin su wurin taimakon kawo zaman lafiya a kananun hukumomin da ake ta’addanci a jihar.
Asali: Legit.ng